An kashe wasu gawurtattun shugababbin ’yan bindiga biyu, Dulhu da kuma Dan Maigari, tare da yaransu sama da 15 a wani rikici da ya barke tsakanin bangarorin ’yan bindiga a Jihar Zamfara.
Kazamin fadan ya kaure ne a safiyar Talata tsakanin bangaren kasurgumin dan bindiga, Bello Turji da wancan bangaren na ’yan bindigar da suka dade ba sa ga-maciji da juna.
- ’Yan bindiga sun kashe ‘Yan sa-kai 30 a Zamfara
- Rikicin APC: Mataimakan Abdullahi Adamu sun bukaci NWC ta juya mishi baya
- Rikicin Yelwa: An sassauta dokar hana fita
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa, “Turji ya yi garkuwa da wadansu mutane, amma mun ji an ce daga baya ya kashe su; an bar gawar Dulhu na da sauran yaransa a maboyarsa.
“Shi kanshi Turji ana kyautata zaton an kashe yaransa a musayar wutar, amma ba a san ko mutum nawa ba ne; amma na ga wadansu daga cikinsu ana komawa da su, dauke da raunin harbi.”
Bangaren Turji da su Dulhu sun yi musayar wutar ne kan zargin kashe wani dan bindiga da ke karkashin wani yaron Bello Turji, wanda ake kira Na-Sanda.
Aminiya ta gano a kan haka ne Turji ya jagoranci yaransa suka kai harin ba-zata a maboyar su Dulhu da ke Maniya, inda suka kashe ’yan bindiga da dama.
Daga cikin ’yan bindigar da su Turji suka kashe har da Dulhu da Dan Maigari, wanda kani ne ga Bashari Maniya, tsohon dan bindiga da yanzu ya zama mai shiga tsakani domin sasantawa tsakanin ’yan bindiga da gwamnati.
Ganau a kauyen Dangondi sun shaida wa Aminiya cewa sun ga ’yan bindiga da dama daga Maniya suna tsallaka babban titin Moriki zuwa Shinkafi, domin tserewa da rayuwarsu, ta cikin dajin Sabubu.
Wakilinmu a Gusau ya nemi samu karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara, SP Shehu Muhammad, amma bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da wakilin namu ya yi mishi ba.