Shugabannin tsaro na ganawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yanzu haka a fadar masarautar Kano.
Ganawar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman ɗarɗar a fadin jihar sakamakon dambaruwar sarauta.
- Sarautar Kano: Muna da yakinin za a yi mana adalci — Aminu Bayero
- Abin da ya sa na fara aikin DJ a Kano — Kyauta Dillaliya
Jam’iyyar NNPP ta soke dokar majalisar ta Kano wacce tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya yi amfani da ita wajen tsige Sanusi II a 2020.
Gwamna Yusuf ya amince da dokar a ranar Alhamis wadda ta rushe sarakunan da aka ƙirƙira tare da ba su wa’adin sa’o’i 48 su fice daga gidajen sarautar.
Sarakuna huɗu sun yi biyayya da umarnin da aka ba su, yayin da Alhaji Aminu Ado Bayero yayi bore tare komawa Kano, inda ya tare a fadar Nassarawa.
Hakan ya fusata gwamnan Kano, inda ya bai wa ‘yan sanda umarnin kama shi, amma umarnin ya haifar da cece-kuce da yamutsi.
Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar rundunar ’yan sandan Kano, a safiyar ranar Asabar, kwamishinan jihar, Usaini Mohammed Gumel, ya ce rundunar za ta yi amfani da umarnin da kotu ta bayar na dakatar da rushe sarakunan.
“Rundunar ‘yan sanda za ta bi umarnin kotu a kara mai lamba FHC/KN/CS/182/2024 ranar 23 ga wagan Mayu, 2024 da babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar ga jami’an tsaro.
“Don haka muna kira ga jama’a da su san cewa ‘yan sanda na aiki tare da sojoji da sauran hukumomin tsaro kuma suna da cikakken ikon samar da tsaro kamar yadda kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya tanada.
“Saboda haka, yayin da rundunar ’yan sanda ke jagorantar sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya, ya kamata a guji tashe-tashen hankula.
“Duk mutumin da aka kama yana ƙoƙarin tayar da tarzoma zai fuskanci fushin doka.”