✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugabannin PDP 10 sun yi murabus a Kano

Shugabannin jam’iyyar a matakin kananan hukumomin sun fice don bin sahun Kwankwaso.

Wasu shugabanni 10 a Jam’iyyar PDP a Jihar Kano sun ajiye mukamansu da zimmar ficewa daga cikinta.

Shugabannin a matakin gunduma a wasu kananan hukumomin jihar sun mika takardar sauka daga mukamansu ga shugabannin kananan hukumomin jam’iyyar a ranar Talata, a yunkurinsu na bin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ke daf da ficewa daga jam’iyyar.

Yayin zantawa da Aminiya, shugaban tafiyar siyasa ta ‘Kwankwaso Kafarka Kafarmu’, Yusuf Bala Usman, wanda ya yi magana a madadin kungiyar, ya ce sun bar PDP ne saboda rashin adalci da aka yi wa ’ya’yan jam’iyyar a yankin Arewa Maso Yamma.

“Mun fice daga jam’iyyar PDP ne saboda rashin bin tsarin dimokuradiyya a jam’iyyar tun daga shiyya zuwa matakin kasa, musamman yankin mu na Arewa Maso Yamma.

“Za mu bi sahun Kwankwaso zuwa kowace jam’iyyar siyasar da zai je saboda mun amince da shi da kuma akidarsa ta siyasa.”

Wadanda suka yi murabus din sun hada da Muhammad Ibrahim, Shugaban Gundumar Rano ta Tsakiya; Nadabo Muhammad, Rano Dawaki; Muhammad Kundu, Rurum Sabon Gari; da Abdullahi Sani, Rurum Tsohon Gari.

Sauran sun hada da Abdullahi Muhammad, Unguwar Yarwa; Saminu Zurgu da Tasiu Muhammad, mazabar Lausu; Saminu Abba, Madachi, Auwalu Falalu, Saji da kuma Muhammad Tukur, Unguwar Zinyau.

Har ya zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto, ba a samu shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi ba, saboda wayarsa a kashe.

%d bloggers like this: