✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin kasuwar Sasa sun yi taron addu’ar cika shekaru biyu

Shugaban kasuwar Sasa a Ibadan, Alhaji Alhassan JK Abubakar ya bayyana cewa a cikin shekaru 2, kasuwarsu ta samu ci gaban da ba ta samu…

Shugaba Alhassan Abubakar ke nan tare da wasu mataimakansa a kasuwar Sasa, Ibadan  Shugaban kasuwar Sasa a Ibadan, Alhaji Alhassan JK Abubakar ya bayyana cewa a cikin shekaru 2, kasuwarsu ta samu ci gaban da ba ta samu irinsa a shekaru 32 da kafuwarta ba.
Shugaban ya fadi haka ne a wata zantawa da ya yi da ’yan jarida a wajen taron addu’o’in zagayowar shekara ta 2 da fara jagorancinsu, a ofishinsa da ke cikin kasuwar ta Sasa.  
Ya zayyana irin ayyukan da suka gudanar don kyautata kasuwar, wadanda suka hada da tsara yanayin tafiyarwa da tsaftace muhalli tare da gina rijiyar burtsatse domin samar da wadataccen ruwa da aikin gina gidajen wanka da makewayi, wanda suka kashe fiye da Naira miliyan 3 kansu.
Ya ce sun sami nasarar hakan ne kuwa saboda kyakkyawar zamantakewar da ke tsakanin al’ummar Hausawa da Yarabawa da suke jan ragamar shugabancin kasuwar. “Dunkulewar da muka yi domin tafiya da murya daya,  ta haifar da kusantarmu da hukumomin Jihar Oyo, wadanda suke ba mu kyawawan shawarwari da tallafi domin bunkasa harkokin kasuwancinmu”. Inji shi.
Shugaba Alhassan, wanda yake tare da wasu mataimakansa (Yarabawa da Hausawa) ya ce, “Mun kafa kwamitocin tsaro da ladabtarwa domin girmama dokokin gwamnati, lamarin da ya haifar da kyakkyawar dangantaka a tsakaninmu da jami’an tsaro. Saboda haka muka bukaci dukkan ’yan kasuwa su tabbatar suna aiki da ka’idodin da muka shimfida domin bin doka da oda da za su taimaka wa samun zama lafiya a cikin kasuwar”.
Daga nan kuma shugaban ya nuna babbar matsalar da suke fuskanta, wadda ta shafi yadda jami’an karbar kudaden haraji da ke tsakanin Ogbomoso zuwa Oyo, suke takura wa direbobin manyan motocin kayan abinci. Saboda haka ya yi kira ga hukuma ta taimaka ta yi maganin wannan matsala, “Kafin ta kai ga kazancewa”. Inji shi.
 Giwan Sasa, Alhaji Rafi’u Akanbi da Shugaban ’yan Albasa na kasuwannin Jihar Oyo, Alhaji Abdul’Azeez Lateef, wadanda suna daga cikin dattawa kuma kusoshi a kasuwar, sun yi bayanai daban-daban na karfafa gwiwa wajen yakar duk abin da zai kawo bambancin kabila ko addini da zai wargaza dadaddiyar dangantakar da ke tsakaninsu. Haka nan sun bukaci gwamnatocin kasa su kara kaimi wajen tabbatar da wanzuwar tsaro.
 Shi kuwa shugaban kwamitin tsare-tsare na kasuwar, Alhaji Salisu Jangebe cewa yayi, a halin da ake ciki kasuwar ta Sasa, ita ce uwa ga dukkan kasuwannin kayan gwari a jihohin Yamma.  Sai kuma ya bukaci gwamnatoci su ba da kara ba da tallafi ga harkokin noman kayan abinci da zai kai Najeriya cikin jerin kasashen duniya da suka ci gaba a harkokin noma.