Shugaban Hamas a Zirin Gaza “mataccen mutum ne” haka sojin Isra’ila suka bayyana a ranar Litinin a daidai lokacin da suka fara abin da ka iya kasancewa shirin hallaka manyan shugabannin kungiyar ce sakamakon harin da aka kai wa Kudancin Isra’ila a ranar Asabar da ta gabata.
Jaridar The Telegraph, wadda ta ruwaito labarin ta ce, gwamnatin Isra’ila ta yi alkawarin farautowa da kashe mayakan Hamas a cikin Zirin Gaza, bayan harin banmamaki da ya hallaka rayukan Yahudawan Isra’ila 700.
Manyan shugabannin biyar su ne:
1. Yahya Sinwar, jagoran Hamas a Gaza, wani matsattsen gari da ke dauke da sama da Falasdinawa miliyan biyu.
“Yahya Sinwar shi ne kwamandan da ya jagoranci hare-haren, don haka a kirga shi a matattu,” in ji Riya Admiral Daniel Hagari, Kakakin Hedikwatar Tsaro ta Isra’ila (IDF).
Ya ce, “Shugabannin Hamas na soji da na siyasa da dukkan dukiyarta za su fuskanci hari kuma a ruguza su.”
Sinwar shi ne babban jami’in Hamas a Gaza, kuma mutum na biyu mafi karfi a Kungiyar Hamas a bayan Isma’il Haniyeh, babban Shugaban Kungiyar.
An haife shi a 1962 a sansanin ’yan gudun hijira na Khan Yunis da ke Kudancin Zirin Gaza.
Yahya Sinwar ya halarci Jami’ar Musulunci ta Gaza inda ya yi digiri a harshen Larabci.
An kama shi a karo na farko lokacin yana jami’a saboda alkarsa da gwagwarmayar Falasdinawa inda aka daure shi kuma ya sha alwashin ci gaba da gwagwarmayar kwato ’yancin Falasdinawa.
A 1988 hukumomin Isra’ila sun tsare shi a kurkuku bisa zargin yunkurin juyin mulki amma aka sake shi a shekarar 2011 – tare da sama da fursunonin Falasdinu 1,000 da aka yi musayarsu da wani sojan Isra’ila mai suna Gilad Shalti da Hamas ta yi garkuwa da shi na tsawon shekara biyar.
2. Mutum na biyu a cikin jerin shugabannin Hamas da Isra’ila ke shirin hallakawa shi ne Mohammed Diefu, shugaban banagren soji na Hamas da ake kira da Birged din Kassam.
A ranar Asabar din ya ce, harin martani ne kan shekara 16 da aka kwashe ana kuntatawa wa Gaza ta hanyar katange yankin daga abubuwan rayuwa da mamayar Isra’ila da kuma jerin abubuwan da suke faruwa a bayan nan na tashin hankali a tsakanin Isra’ila da Falasdinu da suka shafi gineginen gidaje a Yammacin Kogin Jordan da fada a Masallacin Al-Aksa da ke Birinin Kudus.
Falasdina da yawa suna yi masa kirari da zaki saboda yadda yake tunkarar Yahudawan Isra’ila da kuma yadda ya tsallake yunkurin kisa daga kasar Isra’ila.
Ana zargin shi ya kitsa kutsen ranar Asabar, inda mayakan Hamas kimanin 1,000 suka tsallaka iyakar Isra’ila ta Gaza.
Ya shafe shekaru yana yaki da Isra’ila kuma ana zarginsa da shirya hare-haren kunar bakin wake da bama-bamai da suka kashe Yahudwan Isra’ila da dama.
A hankali ya rika ci gaba har ya zama Kwamandan Birged din Kassam. An yi kusan kashe shi a harin jirgin sama shekara 20 da suka gabata, inda ya rasa hannunsa daya da kafa daya.
Kuma ya rasa ido daya a wani harin na Isra’ila. Kuma a shekarar 2014 ne wani harin sojin saman Isra’ila ya hallaka matarsa da dansa jariri.
An ce shi ne ya tsara makamin roka na Kassam, wanda aka harba dubbansa zuwa cikin Isra’ila. Kuma shi ne ya shirya tona hanyoyin karkashin kasa a Gaza.
Ana yi masa lakabi da Deif wato ‘bako’ saboda dabi’arsa ta kwana a kowane dare a mabambanta wurare don kauce wa leken asirin Isra’ila ko hari daga sama.
Deif yana da burin shafe Isra’ila daga bayan kasa. “Deif yana kokarin haddasa yaki na biyu kan ’yancin Isra’ila,” Eyal Rosen, wani Kanar din Sojin ko-ta-kwana na Isra’ila da yake da masaniya da Gaza ya shaida wa kafar labarai ta FT.
Ya ce, “Babban burinsa shi ne -mataki-mataki ya rusa Isra’ila. Wannan ne mataki na farko, wannan farawa ce kawai.”
3. Har wa yau wani babba a jerin da Isra’ila za ta kashe, shi ne Abu Obeida, Kakakin Sojin Hamas. Abu Obeida ne ya sanar da cewa Hamas tana rike da gomman sojin Isra’ila da ta kama a wani ‘wuri mai tsaro’ da kuma ramukan karkashin kasa a Gaza.
Idan hakan ya tabbata, zai zamo abu mai sarkakiya da daukar dogon lokaci wajen tattauna yadda za a yi musayarsu da dubban Falasdinawan da Isra’ila ke tsare da su a gidajen kurkukunta.
4. Babban Shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, wanda yake zaune a wajen Zirin Gaza wato a Katar, zai yi wahala Isra’ila ta kai gare shi.
Wani faifain bidiyo ya nuna Haniyeh a ofishinsa da ke Doha fadar kasar Katar yana murnar harin tare da wasu shugabannin Hamas. Ya bayyana harin da suna Farmakin Ambaliyar Al-Aksa, kuma ya yi alkawarin ci gaba da “yakin kwato kasarmu da fursunoninmu da suke shan bakar wuya a gidajen kurkukun ’yan mamaya.”
Kuma ya ce, Falasdinawa masu dauke da makamai suna da niyyar fadada fadan zuwa Yammacin Kogin Jordan da Jerusalam.
Shi ma ya tsallake akalla yunkurin kisa daga Isra’ila sau daya, inda ya gudu daga Gaza a shekarar 2016 ya koma Qatar.
5. Isra’ila za ta so ta farauto tare da kashe Ziyad al-Nakhalah, Shugaban Kungiyar Jihadin Musulunci (Islamic Jihad).
Kungiyar ba ta tare da Hamas, amma sun hadu wajen kai munanan hare-hare daga Gaza kuma akwai rahoton da ke nuna tana garkuwa da Yahudawa kusan 30.
Al-Nakhaleh, galibi ya fi zama a Beirut, kuma ya fadi ta talabijin a ranar Lahadi da dare cewa, ba za su saki wadanda suka kama ba.