Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga Shugabanni a Afirka da su guji neman tsawaita wa’adinsu a kan mulki fiye a abun da tsarin mulkin kasashensu ya tanada.
A jawabinsa ga taron Majalisar Shugabanni Kasashen Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) Buhari ya kuma yi kira ga shugabannin da su bi dokokin kasashensu wajen gunadar da zabuka masu inganci.
- Shugabannin Arewa na taro kan matsalar tsaron yankin
- Farashin danyen mai ya fadi a kasuwannin duniya
- Kungiyar IPOB ta kashe Hausawa a Jihar Ribas
“Ina kira ga dukkanninmu da cewa kar mu rudu mu bi son ranmu mu nemi dawwamar da kanmu a mulki sabanin abin da kundin tsarin mulki ya tanada.
“Ina jinjina ga wasunmu da suka ki bin irin wannan rudin, kuma za su zama ababen koyi na musamman a kasashenu da ma yankin baki daya.
“Abu na gaba da shi ne muhimmancin tabbatar ingantattun zabuka. Wannan shi ne ginshikin wanzar da tsarin dimokuradiyya a yankin; kazalika wajibi ne bin dokokin kasa.
“Hakan na daga cikin abubuwan da ke haddasa rikicin siyasa da tashe-tashen hankula”, kamar yadda ya yi bayani a taron ECOWAS karo na 57 da ya gudana ranar Litinin a binrin Niamey na Jamhuriyar Nijar.
– Rikita-rikatar shugabancin Mali –
Game da rikicin shugabancin Mali, Shugaban na Najeriya ya yaba wa Shugaban ECOWAS, Shugaban Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar “game da kwazon da ya sa wajen shawo kan matsalar”, tare da Babban Mai Shiga Tsakani, Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
“Najeriya na goyon bayan mastayin ECOWAS na kafa gwamnatin farar hula cikin wata 12 tare da yin komai a bayyane.
“Wannan na da muhimmanci duba da yanayin da ake cikin a Mali, domin masu tayar da kayar baya na iya amfani da yanayin siyasar su jefa kasar cikin wanin babban rikici da ke iya shafar yankin.
“Saurin komawa kan tsarin dimokuradiyya a hannun farar hula a kasar zai samu goyon bayan Najeriya da kuma kaiwa ga janye takunkumin da aka kakaba wa Mali”, inji shi.