Shugaban Kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya katse ziyarar kasashen duniya da yake yi, inda ya koma gida bayan kwanakin da aka yi ana zanga-zangar adawa da gwamnati har aka hallaka akalla mutum 12.
An fara zanga-zangar ce a makon jiya bayan da Mnangagwa ya sanar da karin farashin man fetur da kashi 150.
Yayin da zanga-zangar ta yi kamari, Mataimakin Shugaban Kasar Constantino Chiwenga, wanda tsohon Kwamandan Sojin kasar ne ya kaddamar da wani mummunan farmaki, inda ya sa jami’an tsaro suka harbi masu zanga-zanga da kuma jawo mutane daga gidajensu ana dukansu, kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito kungiyoyin ’yan gwagwarmaya suna fada.