✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban PDP da mabiyansa sun sauya sheka zuwa APC a Nasarawa

Shugaban jam’iyyar PDP na unguwar Gwargwada ta Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC. Shugaban jam’iyyar, Mista Danlami Yanga da…

Shugaban jam’iyyar PDP na unguwar Gwargwada ta Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Shugaban jam’iyyar, Mista Danlami Yanga da mabiyansa sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC a wani taron masu ruwa da tsaki a gudanar a garin Gadabuke.

A cewarsa, “Ni da mabiyane mun yanke shawarar sauya sheka daga PDP zuwa APC saboda salon jagorancin da bamu gano inda aka dosa ba na gwamnatin APC karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Sule da kuma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Balarabe Abdullahi.”

“Ina kiran magoya baya na da kuma mutanen unguwa da su baiwa wannan gwamnati mai ci dukkan goyon bayan da take bukata ta cimma nasarar da ta sa gaba,” inji Mista Yanga.

A kwanan baya ne wani tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar, Madaki Ada-Goje da tsohon Shugaban Karamar Hukumar Gadabuke, Benjamin Belodu, suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.