✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban PDP a Abuja ya rasu a ranar zabe

Yayi hatsarin ne cikin dare bayan taho mu gama da ya yi da wata bishiya.

An shiga rudani yayin da Shugaban Jam’iyyar PDP na Abuja, Sunday Zakka, ya mutu a wani hatsarin mota a safiyar ranar zaben shugaban kasa a Abuja.

Hadimin marigayin, Bawa Benjamin ne, ya tabbatar wa da Aminiya faruwar hatsarin ta wayar tarho.

Ya ce shugaban jam’iyyar ya gamu da ajalinsa ne bayan motarsa ta yi karo wa ta bishiya, a hanyarsa ta dawowa daga wata ganawa da shugabannin jam’iyyar.

Ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2 na dare a yankin Gosa mai nisan kilomita kadan da yankin Kuje da ke Abuja.

Ya ce an garzaya da marigayin zuwa Asibitin Koyarwa na Abuja da ke Gwagwalada, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Shugaban Karamar Hukumar Kuje, Abdullahi Suleiman Sabo, ya tabbatar da rasuwar shugaban jam’iyyar ga wakilanmu.