✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban NFF ya je ta’aziyyar tsohon dan wasan Kano Pillars

Marigayin ya wakilci Najeriya a Gasar Cin Kofin Duniya na matasa ’yan kasa da shekara 20

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) Ibrahim Musa Gusau ya je Kano domin ta’aziyyar tsohon dan wasan Najeriya da kuma Kungiyar Kano Pillars, Mohammed Bello Kofar Mata.

Ya kai ziyarar ta’aziyyar ce ga ’yan uwa da iyalan tsohon dan wasan a gidansu marigayin da ke unguwar Kofar Mata a birnin Kano ranar Lahadi.

Kakakin Kungiyar Daliban Kofar Mata, Usman Bello, wanda aka yi ziyarar a idonsa ya shaida wa Aminiya cewa, bayan jajanta wa iyalai da ’yan uwan marigayin, Shugaban na NFF ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa.

Mohammed Bello Kofar Mata Ya rasu ne bayan gajeriyar jinya, a makon jiya.

A lokacin rayuwarsa, ya wakilci Najeriya a Gasar FIFA ta Cin Kofin Duniya na matasa ’yan kasa da shekara 20, gami da kungiyar Kano Pillar wasu kulob-kulob na cikin gida.

Cikin wadanda suka raka Shugaban na NFF, har da Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Jihar Kano, Alhaji Sharu Rabi’u Ahalan da sauran jami’an kula da harkokin wasanni na jihar.