Shugaban kamfanin Media Trust, mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Kabiru Yusuf, ya zama sabon Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Jarida ta Najeriya (NPAN).
Malam Kabiru Yusuf ya samu matsayin ne a lokacin babban taron kungiyar na shekara-shekara na 2020 a Sakatariyarta da ke Legas.
- APC ta rusa shugabanninta a dukkan matakai
- Asirin budurwa ya tonu bayan saurayi ya yi garkuwa da ita
- Uwa ta rataye ’ya’yanta 2 don ta yi lalata da kare
Shugaban NPAN mai barin gado, Nduka Obaigbena ya gabatar da kudurin zaben Malam Kabiru, inda ya samu amincewar Mis Comfort Obi mai mujallar The Source Magazine.
A jawabinsa, Malam Kabiru ya yaba wa shugabannin kungiyar masu barin gado tare da neman hadin kan ’yan kungiyar.
Shugabannin masu barin gado “sun tabbatar da ganin mun samu sakatariya, mu kuma za mu yi bakin kokarinmu domin ganin sakatariyar na aiki yadda ya kamata”, inji shi.
Taron na NPAN ya kuma zabi mai gidan jaridar Guardian, Uwargida Maiden Alex-Ibru a matsarin Mataimakiyar Shugaba; sai mai jaridar BluePrint, Mohammed Idris a matsayin Babban Sakatare.
Sauran sun hada da mai jaridar The Nation, Walter Edun, Ma’aji; Misis Mwadiuto Iheakanwa ta jaridar Champions, Sakatariyar Watsa Labarai; Manajan Daraktan jaridar Daily Times, Fidelis Anosike kuma Mataimakin Sakataren kungiyar.
Su kuma Prince Dannis Sami na The Pilot; da mawallafin jaridar Leadership, Sam Nda-Isaiah; da kuma tsohon shugaban kungiyar, Ray Ekpu, an zabe su a matsayin shugabanni na alfarma ba tare da hamayya ba.
Shugaban kungiyar mai barin gado kuma, Obaigbena, taron ya zabe shi a matsayin uban kungiya har iya tsawon rayuwarsa saboda kwarewarsa.