Yayin da al’ummar ƙasar nan ke fama da tsadar rayuwa, musamman a ɓangaren kayan abinci da sutura, a iya cewa kusan komai na rayuwa a ƙasar nan na neman fin ƙarfin talaka.
Hakan kuma bai rasa nasaba da irin matakan farfaɗo da tattalin arziki da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka, na gyara tattalin arzikin ƙasa.
- An tsare wata mata kan zargin kashe ’yarta da maganin ɓera a Kaduna
- Gobara: Gwamnatin Yobe ta tallafa wa ’yan kasuwar Damaturu da Gashua
Gwamnatin, ta bayyana da cewa, ya durƙushe gaba ɗaya, kuma ya zama dole ta ɗauki mataki don ganin an daidaita al’amura, wanda hakan ya jefa al’umma cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
Tun bayan janye tallafin man fetur da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, farashin komai ya tashi, sannan kuma ga faɗuwar darajar Naira, wanda hakan ya sake ta’azzara halin da jama’a suka tsinci kansu a ciki na ƙarin ƙuncin rayuwa.
Lafiya dai an ce uwar jiki, kuma sai da lafiya ake komai, to shi kansa wannan ɓangare na harkar lafiya, shi ma ya samu nasa kason a fannin tashin gwauron zabo, inda tsadar magunguna a asibitoci ta sa marasa lafiya da ’yan uwansu suka koma sayen maganin a hannun masu tallan sa a kafaɗa, ko amfani da magungunan gargajiya.
Farashin magunguna a asibiti na ci gaba da tashin gwauron zabo a ƙasar nan, lamarin da ke ƙara jefa marasa lafiya da ’yan uwansu cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
A sakamakon haka ne, marasa lafiya da dama sukan koma amfani da abin da ya fi musu sauƙi ko dai sayen maganin a hannun masu tallan sa a kafaɗa ko amfani da maganin gargajiya ko kuma a wasu lokutan, su haƙura da maganin ɗungurungum.
Aminiya ta yi nazari a kan halin da marasa lafiya suka shiga, sakamakon tashin gwauron zabo da maganin asibiti ya yi.
Me hakan ke nufi ga wanda sai ya fita, kafin ya samu abin da zai ciyar da iyalansa?
Me zai faru ga wanda wata rashin lafiya ta same shi, kuma bai da halin sayen magani?
Wane mataki gwamnati ta ɗauka domin sauƙaƙa wa al’umma a harkar lafiya?
Wani bincike da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, mafi akasarin al’ummar ƙasar nan na biyan kuɗin asibiti ne daga aljuhunsu, walau ta albashinsu ko kuma abin da mutum yake samu.
Wasu marassa lafiya da Aminiya ta tattauna da su, sun bayyana cewa, suna shan wahala domin “duk maganin da aka rubuta maka, za a ce ka je ka saya, kuma idan ka je wajen sayar da maganin sai tsada, sai ka sayi magani yau misali Naira 1000, amma gobe idan ka koma sayen irin wannan maganin, sai ka ji farashin ya haura fiye da yadda ka saya jiya.
“Mu masu fama da cutar siga muna fama da wahala sosai a kan tsadar maganin, domin likita zai rubuta maka maganin kamar na kwana bakwai.
“To idan ka je saye kamar yadda na ce yau ka saya Naira 1500, to idan ka koma sayowa za a ce maka kuɗin maganin ya ƙaru, ya koma Naira 2500, to kai kuma ka je da Naira 1500 kuma ba ka da cikon kuɗin, yaya mutum zai yi, ai ka ga mutum ya shiga cikin wani hali. Gaskiya magunguna sun yi tsada sosai.”
A cewarsa, “gaskiya babu wasu magunguna da za ka iya sauyawa da wanda likita ya rubuta maka, domin yin hakan kan iya jefa mutum cikin wani hali na daban, sai dai kawai idan ba ka da kuɗin sayen magungunan, sai ka yi ƙoƙarin kiyaye abubuwan da aka hana ka ci ko yin amfani da su, to muddin ka ce za ka canza wasu magungunan da wanda ba likita ne ya rubuta maka ba, to tabbas akwai matsala”.
Maras lafiyar ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka, ta samar musu da magunguna a cibiyoyin da za a same su da sauƙi a matakin farko, domin yin hakan zai taimaka wa masu fama da wannan cuta ta ciwon siga, kuma za a samu nasarar ceto rayukan jama’a da dama.
Shi ma wani maras lafiyar cewa ya yi ba su da yadda za su yi, domin maganin na neman fin ƙarfinsu, illa kawai su koma shan na gargajiya. Ya koka a kan cewa, “maganar gaskiya gwamnati sam ba ta kyautawa, ta yaya za a lafta haraji a kan magani, haba ai ya kamata a sausauta.
“Yanzu haka da ka je shagon sayar da magani, sai ka ji an ce maka kuɗin maganin Naira 5000, a ina za mu samu kuɗin sayen a matsayinmu na talakawa da sai mutum ya fita aiki, ya samo abin da zai ciyar da gidansa, dole na haƙura, na koma shan na gargajiya, Allah ne Yake ba mu lafiya, domin abin sai haƙuri.
“Don Allah gwamnati a duba mana lamarin magani ɗin nan a taimaka mana.”
Hauhawar farashin magunguna ta sa marasa lafiya neman wata hanya ta samun lafiya, kuma jama’a da dama cikin fargaba.
Dalilin tsadar
Shin mene ne ya jawo tashin farashin magungunan?
Mista Onyeka Chinedu da Mista Aki Chimade wasu masu shagunan sayar da magani, sun bayyana cewa, sun danganta hakan da yadda al’amura suka yi tsada a ƙasar nan, “domin su kansu kamfanonin yin magungunan suna da ma’aikatan da suke biyan su albashi a kowane wata, kuma dole ne su biya su, sannan suna yin wannan harka ne domin samun riba, babu ta yadda za a yi ka kai kayanka kasuwa, ka yi asara don kawai kana son burge mutane.
“To haka lamarin yake ga kamfanonin harhaɗa magungunan, dole su tabbatar sun samu riba ba asara ba. Hakazalika su masu sayar da magungunan a shago dole ne idan ka sayo magani, ka tabbatar da abin da za ka samu.
“Wani lokaci za ka sayo kayan farashin da ka sayo a baya, amma da zarar ka sake yin odar kayan, sai kaji wani sabon farashin da ya zarce tunaninka, sannan ga tsadar kuɗin motar da za ta ɗauko maka kayan.
“To kai a matsayinka na ɗan kasuwa dole ka yi komai cikin lissafi, don ka samu kuɗinka, ya dawo ko da ba ka samu wata riba mai yawa ba.
“Hakan takan sa dole mu ƙara kuɗin magungunan kamar yadda muka sayo shi, domin ana yin komai domin samun riba ce.
“Sannan wata babbar matsala, akwai kamfanonin yin magungunan da suka rufe za su bar ƙasar nan, saboda yadda al’amura suke tafiya, wanda wannan ya taimaka sosai wajen tsadar magungunan, sannan magungunan sun yi ƙaranci a kasuwanni, kuma ko ka samu maganin za ka sayo shi da tsada sosai.
“To ka ga dole ka san yadda kai ma za ka fitar da ribarka. Maganin da a da muke saye Naira dubu 15 a yanzu za ka same shi ya haura Naira dubu 30.
“Hakan ta sa mafi yawan marasa lafiya suke neman wata hanya ta taimakon kansu, ta komawa sayen magunguna masu sauƙi duk da aikinsu ɗaya ne.”
“Haƙiƙa ƙarin farashin man fetur da hauhawar farashin Dala da ƙarin kuɗin sinadarin haɗa magunguna na daga cikin abubuwan da suka sa magungunan suka yi tsada.
“Gaskiya ya kamata gwamnati ta shigo cikin lamarin nan, domin komawa shan magungunan gargajiya na da tasa illar, ba kamar na Bature ba, akwai ƙa’idar lokacin shan sa, amma na gargajiya wasu na sha da ka ne, wanda hakan yana da hatsari sosai.
“Maganar ita ce tunda magunguna suka yi tsada, ba kowa ne yake iya sayen magani ba.
Ɗabi’ar shan magunguna haka kawai za a iya cewa ta zama ruwan dare, to amma yadda tsadar magungunan take ta sa ala dole mutane masu waccan ɗabi’ar suka yi watsi da hakan, domin hatta masu fama da cututtuka na neman ƙaurace wa shan maganin Turawa, sun koma shan na gargajiya domin samun waraka.