Wani bincike da jaridar Daily Trust ta yi, ya gano cewar aƙalla jami’an ’yan sanda 229 ne, suka rasa rayukansu tsakanin watan Janairun 2023 zuwa watan Oktoban 2024.
Sun rasu ne sakamakon hare-haren ’yan bindiga, ’yan fashi, ’yan ƙungiyar asiri, da kuma masu aikata laifi.
- Dokar gyaran haraji ba za ta cutar da Arewa ba – Fadar Shugaban Ƙasa
- HOTUNA: Gidaje 753 da EFCC ta kwace a hannun jami’in gwamnati
Wasu kuma sun mutu ne a hannun gungun jama’a.
Wani lamari mai tayar da hankali shi ne na ASP Augustine Osupayi a Legas, wanda gungun jama’a suka kashe yayin da yake ƙoƙarin tabbatar da doka a watan Oktoban 2024.
Wani ɗan sanda mai suna Abdul ya ce: “Duk wanda ya mutu wajen yi wa ƙasarsa hidima jarumi ne.
“Wannan ba zai hana mu ci gaba da aikinmu ba.”
Wani ɗan sanda mai suna Ndifrike, ya ƙara da cewa: “Muna nan daram, amma hukumar ‘yan sanda ta kula da iyalanmu idan wani abu ya same mu.”
Masani kan harkokin tsaro Abdullahi Garba, ya buƙaci Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, ya bai wa jami’ai kayan aiki na zamani don kare kansu.
Wani masani kan harkokin tsaro, Silas Daves, ya nemi haɗin kai tsakanin ’yan sanda da kuma inganta tattara bayanai don hana kai musu farmaki.
Duk da haka, wani babban jami’i a hedikwatar ’yan sanda, ya ce suna gudanar da bincike kan kisan jami’an.
Ya ƙara da cewa: “Za mu yi bincike tare da gano dalilan da suka haifar da kashe waɗannan jami’an.”
Haka kuma, wasu jami’ai sun yi kira ga rundunar ’yan sanda da ta ƙara kula da jin daɗin jami’an da suka rage, domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu duk da barazanar da rayuwarsu suke fuskanta.