✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Majalisar Filato da mataimakinsa sun yi murabus

Wannan dai na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta kwace kujerar gwamnan jihar

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Filato, Moses Thomas Sule, ya yi murabus daga mukaminsa.

Kazalika mataimakinsa, Gwottaon Fom, shi ma ya ajiye mukaminsa.

Bayan haka ne aka zabi dan majalisa mai wakiltar Pankshin ta Arewa Gabriel Dawang, a matsayin sabon shugaban majalisar.

Honorabul Timothy Dantong mai wakiltar mazabar Riyom kuma a yanzu shi ne sabon mataimakin shugaban majalisar.

Aminiya ta ruwaito cewa hakan na da nasaba da kwace kujerar gwamnan jihar, Caleb Mutfwang da wasu ’yan majalisar dokokin jam’iyyar PDP da kotu ta yi.

%d bloggers like this: