Wani mutum ya tsinci kansa a gidan yari bayan an kai shi kotu bisa zargin yi wa wata ’yar shekara 50 fyade.
Babbar kotun jihar Edo ce ta tasa keyarsa zuwa gidan yari zaman sauraron hukunci.
Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wanda ake tuhuma ya musanta zargin da ake masa na yunkurin yi wa dattijuwar mai shekara 50 da haihuwa fyade.
- ’Yan bindiga sun bukaci N900m kudin fansar mutane 13 da suka sace a Abuja
- DAGA LARABA: Dalilan Da Za A Hana ’yan kasa da shekara 18 shiga jami’a
Lauya mai shigar da kara, Misis Ama Iyamu, ta shaida wa kotun cewa a ranar 27 ga Maris, 2023, a birnin Benin ne wanda ake zargin ya yi yunkurin yi wa matar fyade.
Barista Iyamu ta ce, wannan laifi ya saba wa sashe na 4 na dokar cin zarafin jama’a ta jihar Edo, ta 2021, kuma laifin na da hukunci a sashe na 5 (2) na wannan doka.
Bayan sauraron karar ne Mai Shari’a Efe Ikponmwonba, ta bayar da umarnin a tsare wanda ake zargi a gidan yari
Ta kuma dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Yuli 2024.