✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan sama ya lalata gidaje 200 da makarantu a Filato

Guguwa da mamakon ruwan sama sun ɗage rufin gidaje kimanin 200, asibitin ajujuwa da shaguna a yankin Miango

Aƙalla gidaje 200 da ajujuwan makarantu da asibitoci ne suka lalace bayan mamakon ruwan sama a gundumar Miango ta Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato a yammacin ranar Litinin.

Sakataren yaɗa labarai na Ƙungiyar Cigaban Matasan Miango, Nuhu Bitrus Nga, ya ce mutane uku kuma sun jikkata a lokacin ruwan kuma suna karɓar magani a asibiti.

“Guguwar da ruwan saman sun kware rufin gidaje kimanin 200 da asibitoci da ajujuwa da shaguna da kuma gidajen dabbobi.

“Ta tumɓuke itatuwa, ta raba mutane da dama da matsugunansu, baya ga asarar dukiya mai tarin yawa.

“A halin yanzu, wasu mutanen da abin ya shafa sun sami mafaka a gidajen maƙwabta.

“Amma barnar da mamakon ruwan sama ya haifar ya ƙara jefa al’ummar Miango da suka sha fama da munanan hare-hare da kuma gudun hijira a cikin wani mawuyacin hali,” in ji Nga.

Al’ummar yankin sun yi kira ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), majalisar karamar hukumar, da jungiyoyi masu zaman kansu da masu hannu da shuni da su kawo agaji ga wadanda abin ya shafa.

Yadda ruwan saman ya lalata wasu makarantu a Filato hoto daga Channelstv.com