✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Majalisar Dattawa ya shiga jerin masu neman takarar shugaban kasa a APC

Na dogara ga Allah Madaukakin Sarki kan wannan tafiya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Sanata Lawan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja, yayin da ya ke karbar takardun bayyana manufar neman takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar mai mulkin kasar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wata kungiyar siyasa mai suna ‘National Stability Project’ karkashin jagorancin, Cif Sam Nkire ce ta fitar da naira miliyan 100 wajen saya masa fom din neman takarar.

Wasu rahotanni kuma sun bayyana cewa, daga cikin wadanda suka bayar da gudunmuwar saya masa fom din takarar har da wasu daga cikin ’yan majalisar Tarayya da suka hada da;  Sanata Bello Mandiya da Sanata Barau Jibrin da Sanata Yusuf A. Yusuf wadanda suka je har sakatariyar jam’iyyar domin sayen fom din.

Sanatan ya ce ya saurari kiraye-kirayen da aka yi masa kan neman ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa kuma yana mai amsa wannan kira.

“Ina so in mika kaina ga wannan kira da aka min, wannan ba tafiyata ba ce, wannan tafiyarmu ce domin kowane hannu dole ne ya kasance a kan tudu don kai kasar nan zuwa mataki na gaba,” in ji shi.

A cewarsa, duk da ya shiga takarar a makare ganin yadda ‘yan takarar shugaban kasa ke da yawa a APC, amma yana mai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba.

“Zan yi komai cikin tsari kuma bisa ka’ida, ba zan saba ka’ida ba, haka nan ba zan saba wa ka’idar jam’iyyarmu ba.

“Na dogara ga Allah Madaukakin Sarki kan wannan tafiya,” in ji shi.