✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban La Liga ba ya kaunar Barcelona —Laporta

Duk wanda ke kokarin zubar da mutuncin kungiyar nan, sai inda karfin mu ya kare.

Joan Laporta ya ce ba zai ajiye aikin shugabancin Barcelona ba, domin abin da Javier Tebas ke fata kenan.

Ranar Litinin Tebas ya ce ya kamata Laporta ya yi murabus idan har ya kasa fayyace wasu kudi da aka biya Jose Maria Enriquez Negreira, tsohon shugaban kwamitin alkalan tamaula a Sifaniya.

“Wannan hukunci ne daga wajen mambobi kan shugabansu,” in ji laporte kamar yadda ya fada ranar Talata.

An zabi Laporta da yawan rinjaye a Maris din 2021.

“Duk wanda ke kokarin zubar da mutuncin kungiyar nan, sai inda karfin mu ya kare.”

Laporta ya fada cewar Tebas shugaban La Liga “baya kaunar Barcelona.”

Takaddama ta tashi ne ranar Laraba da ta gabata kan biyan fam miliyan 1.2 ga kamfanin Negreira tsakanin 2016 zuwa 2018.

Daga baya aka bankado cewar kungiyar ta biya mai shekara 77 kudi Yuro miliyon 7 tsakanin 2001 zuwa 2018, shekarar da ya bar mukamin shugaban kwamitin alkalan tamaula.

Barcelona wadda rabonta da La Liga tun bayan kaka hudu, tana ta daya a teburin bana da tazarar maki takwas tsakaninta da Real Madrid ta biyu.

Sai dai wasu na shakku kan kwazon Barcelona ko makomarta kan wannan batun da ta musanta.