Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Hukumar Kula da Cigaban Neja Delta (NDDC), Olubunmi Tunji-Ojo ya sauka daga mukaminsa.
Olubunmi Tunji-Ojo ya sauka daga mukaminsa ne a ranar Litinin, yayin da kwamitin ke ci gaba da sauraron bayanai kan zargin badakalar Naira biliyan 81.5 a hukumar.
Kwamitin rikon NDDC karkashin Farfesa Kemebradikumo Pondei ya bukaci shugaban kwamitin ya ajiye mukaminsa, a lokacin Farfesa Pondei da Ministan Neja Delta Godswill Akpabio suka bayyana a gaban Kwamitin wanda ya ba su wa’adin ranar Litinin din domin amsa tambayoyi.
In ba a manta ba, a makon jiya kwamitin rikon na NDDC ya fice a lokacin da ake tsaka da zaman kwamitin majalsiar, bisa zargin shugaban kwamitin majalisar da yi wa hukumar bi-ta-da-kulli da kuma saba doka.