✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Kwamitin Kafa Rundunar Tsaro a Sakkwato Ya Yi Murabus

Shugaban kwamitin kafa rundunar tsaro ta Jihar Sakkwato, Kanar Garba Moyi mai ritaya ya yi murabus kwana biyar bayan kafa kwamitin.

Shugaban kwamitin kafa rundunar tsaro ta Jihar Sakkwato, Kanar Garba Moyi mai ritaya ya yi murabus kwana biyar bayan Gwamna Ahmad Aliyu ya kafa kwamitin.

Kanar Moyi ya shaida wa ’yan jarida cewa ya yi murabus ne sakamakon sukan da yake sha daga  mutanen da nadin nasa  bi yi wa dadi ba, domin a samu zaman lafiya.

Ya ce, “Allah ne kawai Ya san dalilinsu, na sadaukar da rayuwata a wurin aikin soja na gama lafiya, na shiga siyasa a zabe ni shugaban karamar hukumar Isa, na zama kwamishinan tsaro har sau uku ni naje aikin kwamishina da kaina.

“Wannan aikin da aka ba ni an yi haka ne don ganin na cancanta amma saboda wasu dalilai da wasu ke gani abin ya ba su tsoro suka rika amfani da wasu kafofi suna bata min suna don haka na ga ya cancanta na ajiye mukamin,” in ji Garba Moyi.

Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya amince da kafa na mutu 25 domin su kirkiro hukumar tsaron al’umma ta Sakkwato.

Kwamitin na karkashin jagorancin Kanal Garba Moyi da Alhaji Yusha’u Muhammad Kebbe mataimakin shugaba da barista Gandi Umar matsayin Sakatare.

Ayyukan da Gwamna Ahmad ya ba wa kwamitin, kamar yadda mai magana da yawunsa Abubakar Bawa ya sanar su ne: bayar da shawara kan yadda za a samar da hukumar, ayyukanta, karfin ikonta da kuma hanyoyin samun kuden gudanawarta.

Sauran su ne daukar ma’aikata, ba su horo, rantsar da su, da kuma wayar da kan jama’a kan ayyukan hukumar a kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar.

Ko da yake takardar ba ta bayyana wa’adin da aka baiwa kwamitin ba don ya kammala aikinsa.

Masu sharhi na ganin kafa kwamitin da gwamnatin Sakkwato ta yi, koyi ne da Gwamnatin Jihar Katsina wurin samar da jami’an tsaronta da za su yi aiki tukuru don samar zaman lafiya a cikin jihar.