Shugaban hukumar kwallo kafar Sifaniya Luis Rubiales ya ajiye mukaminsa kan cece-kucen sumbatar wata ’yar wasa ta tawagar matan kasar.
Rubiales ya ajiye aikin ne ranar Lahadi mako uku bayan an zarge shi da sumbatar ’yar wasan ba tare da izininta ba.
Ya sumbaci ‘yar wasa Jenni Hermoso ta tawagar kwallon kafar mata ta Sifaniya yayin da suke murnar lashe Kofin Duniya na Mata a watan jiya.
Rubiales ya sanar da sauka daga mukaminsa ne a wata sanarwa da ya fitar yana mai cewa ba zai iya ci gaba da rike mukamin ba a Hukumar Kwallon Kafar Sifaniya (RFEF) sannan daga bisani ya tabbatar da cewa ya mika takardar ajiye aiki ga shugaban riko na hukumar Pedro Rocha.
Kazalika Rubiales ya sauka daga matsayinsa na mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar Turai UEFA.
Kusan mako biyu da suka gabata, Luis Rubiales ya gabatar da wani jawabi cike da bijirewa inda ya jaddada cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba duk da matsin lambar da ake yi masa.
Maimakon neman afuwa kan abin da ya aikata, ya dage cewa ‘yar wasan da ya sumbata Jennifer Hermoso, ta amince ya sumbace ta.
Amma tun bayan jawabin nasa, FIFA ta dakatar da shi daga mukaminsa, sannan hukumar kwallon kafar Sifaniya ta nemi ya ajiye aiki, kana Hermoso ta gurfanar da shi a kotu, sannan mahaifiyarsa, wadda da farko ta soma yajin cin abinci saboda batun, ta daina.
Hermoso ta ce ba ta ji dadi ba lokacin da Rubiales ya sumbace ta kuma ba ta amince da hakan ba. Ta kara da cewa ya rika matsa mata lamba domin ta gaya wa duniya cewa ya sumbace ta ne bayan ta amince da hakan.
Yayin da yake ajiye aikinsa, Rubiales ya jaddada cewa an rika shirga karya game da abin da ya aikata.