✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Kasa ya kori Firaiminista a Somaliya kan badakalar filaye

Lamarin dai ya dada dagula rikicin siyasar kasar.

Shugaban Kasar Somaliya, Mohamed Abdullahi Mohamed, ya sanar da korar Firaiministan kasar, Hussein Roble daga bakin aiki, a daidai lokacin da shugabannin biyu ke ci gaba da yin zaman doya da manja a tsakaninsu.

Takun sakar dai ta sa shugabannin biyu nuna wa juna yatsa da zargin juna kan ci gaba da dage zaben Majalisar Dokokin kasar.

Matakin na Shugaba Mohammed na ranar Litinin dai ya dada dagula al’amuran rikicin siyasar da kasar ta tsinci kanta a ciki na tsawon watanni, lamarin da kuma ya dada fargabar da ake yi ta yiwuwar fuskantar rikici.

“Shugaban Kasa ya yanke shawarar korar Firaiminista tare da janye duk wani ikonsa, tun da ana zarginsa da rashawa,” a cewar wata sanarwa da ofishin Shugaban Kasar ya fitar ranar Litinin.

Shugaba Mohammed dai na zargin Firaiminista Hussein ne da yin katsa-landan a binciken da ake yi masa na hannu a wata badakalar filaye a kasar.

Sanarwar ta kuma ce ana binciken kwamandan tashoshin ruwan kasar, wanda shi ma aka kora saboda zarge-zargen rashawar.

To sai dai a cikin martaninsa, Firaiminista Hussein ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, matakin wani yunkuri ne na yin juyin mulkin soja, kuma ya saba doka.

Ya kuma ce yana nan kan bakarsa wajen sauke nayuin da doka ta dora masa na shirya karbabben zaben da zai kawo karshen dambarwar siyasar kasar.

Kasar Somaliya dai, wacce ke da iya Gwamnatin Tarayya kawai tun shekarar 1991, a yanzu na kokarin sake gina kanta tare da taimakon Majalisar Dinkin Duniya wajen yaki da mayakan Alka’ida da na Alshabab.