✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban juyin mulkin Mali ya karbi kundin tsarin mulki

Sojojin sun yi alkawarin gudanar da zabe a watan Fabrairun 2024 da kuma mika wa zababbiyar gwamnati mulki a watan Maris

An mika wa shugaban sojojin da suka yi juyin mulki a Mali, Assimi Goita, daftarin kundin tsarin mulkin kasar, a wani mataki da ake zargin yunkuri ne na ci gaba da zamansu a kan mulki zuwa 2024.

Kawo yanzu dai ba fitar da daftarin kundin tsarin mulkin ba ga jama’a kuma an mika shi ne wata biyu bayan wa’adin da aka sanya, bayan shugaban kwamitin ya ce an kara wa’adin.

Shugaban gwamantin rikon, Fousseyni Samake ya gargadi Goita cewa, “Duk kundin tsarin mulkin da aka rubuta sai an kalubalance shi sannan sai ya haifar da rudani.”

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali wadda sojojin da suka mamaye tun 2020, sun bayyana bukatar samar da daftar kundin mulkin da zai kunshi sauye-sauyen da ake bukata domin daidaita kasar.

A watan Yuni ne gwamnatin ta kafa kwamitin bayan ta tsawaita wa’adin shguabanin sojojin zuwa shekarar 2024, tare da cewa za a yi zaben raba-gardama kan kundin tsarin mulkin.

Bayan shan matsin lamba, sojojin sun yi alkawarin gudanar da zabe a watan Fabrairun 2024 da kuma mika wa zababbiyar gwamnati mulki a watan Maris.