Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya lashe lashe kyautar shekarar 2020 ta Dala ta Gidauniyar Mo Ibrahim na shugabancin Afirka.
Kwamitin bayar da kyaututtukan ya yaba wa shugabancin Shugaba Mahamadou Issoufou a Nijar, daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya.
- An ci gaba da sauraron shari’ar ‘bidiyon Dala’ na Ganduje
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 19 a Neja
- Mayakan Houthi sun harba makami mai linzami cikin Saudiyya
- Kungiyar OPC ta kone kauyen Fulani ta kashe mace mai ciki a Oyo
Kwamitin ya ce, shguaban “ya inganta bunkasar tattalin arziki, ya nuna jajircewa wajen tabbatar da daidaito a yankin da kuma tsarin mulki, da kuma karfafa dimokiradiyyar Afirka.”
Shugaban ya yi wa’adi biyu na shekaru biyar a matsayin shugaban kasa daga 2011 wanda yanzu Tsohon Ministan Cikin Gida, wanda ya lashe zaben shugaban kasar a watan jiya, Mohamed Bazoum ne zai gaje shi.
Mista Issoufou wanda shi ne mutum na shida da ya samu lambar yabo ta Mo Ibrahim, ya wallafa ce kyautar ta karrama dukkan mutanen Nijar.
“Na dauki wannan lambar yabo a matsayin karfafa gwiwa don ci gaba da yin tunani da aiki a hanyar da za ta bunkasa kimar dimokiradiyya da kyakkyawan shugabanci, ba wai a Nijar kadai ba, har ma da Afirka da ma duniya baki daya.”
Sauran wadanda suka samu kyautar su ne:
- Tsohuwar Shugaban Liberia, Ellen Johnson Sirleaf ta Liberia (2017)
- Shugaba Hifikepunye Pohamba na Namibia (2014)
- Shugaba Pedro Pires na Cabo Verde (2011)
- Shugaba Festus Mogae na Botswana (2008)
- Shugaba Joaquim Chissano na Mozambique (2007).