✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Hukumar Aikin Hajji na Kaduna ya rasu a hadarin mota

Shugaban Hukumar Aikin Hajji na jihar Kaduna Alhaji Sani Dailhatu Musa, ya rasa ransa a hanyar Kaduna zuwa Abuja. Hadarin wanda ya auku da safiyar…

Shugaban Hukumar Aikin Hajji na jihar Kaduna Alhaji Sani Dailhatu Musa, ya rasa ransa a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hadarin wanda ya auku da safiyar yau Laraba akan hanyarsu ta zuwa taro a Abuja ya faru ne da misalign karfe 10 na safe.

Aminiya ta samu labarin su uku ne a cikin motar da direban, amma shi kadai Allah Ya yi wa cikawa zuwa yanzu.

Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar Salisu Sani Anchau, ya tabbatar da rasuwar.

Ya ce, dukkansu an kaisu wani asibiti da ke Abuja, inda aka tabbatar da rasuwarsa.