Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo, ya nada Firamistar Kasar, Rose Christiane Ossouka Raponda, a matsayin mataimakiyarsa.
Da wannan, Rose ta zama mace ta farko da taba riki wannan mukamin a tarihin kasar.
Da kuma ita ce mace ta farko a kasar da ta taba rike mukamin Firaminista.
Kafin nadain nata, Roce ce Firaministar kasar, haka nan Ministar Tsaro.
Tsohuwar Ministar Tsaron, mai shekaru 59, wacce aka nada a mukamin Fira Minista a watan Yulin 2020 bayan wanda ya gabace ta ya yi murabus, yanzu ta zama mataimakiyar Shugaban Kasa duk da cewa mukamin bai ba da damar yin aiki na wucin-gadi a matsayin Shugaban Kasa ba.
Tuni dai Shugaban Kasar ya maye gurbin Rose da tsohon minista Alain-Claude Bilie-By-Nze, a matsayin sabon Firaministan kasar kamar yadda Babban Sakataren gwamnatin kasar, Jean-Yves Teale ya bayyna cikin bidiyon da aka wallafa a shafin Twitter na Shugaban Kasar.