✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Faransa ya kai ziyara Saudiyya

Mista Macron ya mayar da martani da cewa ziyarar da ya kai ba ta nufin ya manta da kisan Khashoggi.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya kai ziyara Saudiyya inda zai gana da yarima mai jiran gado na kasar, Mohammed Bn Salman.

Ziyarar da Shugaba Macron ya kai Saudiyya ranar Asabar na daya daga rangadin da yake yi a kasashen yankin Gulf.

Rahotanni sun ce Mista Macron da Yarima Salman za su tattauna batutuwan da suka shafi yankin ciki har da rikicin kasar Lebanon da kuma dakatar da tattaunawar nukiliya da Iran.

Tattaunawa tsakanin Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Yarima mai jiran-gado na Saudiyya, Mohammed Bn Salman

Ziyarar Shugaban na Faransa ita ce ta farko da wani shugaba daga manyan kasashen yammacin duniya ya kai wa Saudiyya tun bayan kisan gillar da aka yi wa dan jaridar Saudiyya kuma marubucin jaridar Washington Post, Jamal Khashogi a shekarar 2018.

Mista Macron ya mayar da martani kan korafin wasu kungiyoyin kare hakkin bil Adama suke yi, inda ya ce ziyarar da ya kai ba ta nufin ya manta da kisan Khashoggi da aka yi shekaru uku da suka gabata.

Shugabar Kungiyar Amnesty International, Agnes Callamard, ta zargi Mista Macron da zubar da darajar kansa da kuma kasarsa.

Kisan Khashoggi ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin kasashen duniya da ke ci gaba da ta da jijiyoyin wuya.

Tuni dai Saudiya ta musanta cewa ita ta bayar da umarnin kisan Mista Khashoggi a kasar Turkiyya.