✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban APC a Jihar Binuwai ya rasu

Shugaban APC na Karamar Hukumar Ukum ya mutu bayan rashin lafiya.

Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Ukum ta Jihar Binuwai, Tony Aboh ya rasu.

Shugaban jam’iyyar a Jihar, Abba Yaro, ya bayyana cewar Aboh ya rasu ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

“Labarin mutuwarsa ya girgiza mu, duba da irin yadda yake da himma wajen hada kan al’umma.

“Muna mika sakon gaisuwa ga iyalansa da daukacin jama’ar Karamar Hukumar Ukum bisa wannan rashi,” a cewar Yaro wanda ya fitar da sanarwar a madadin Kwamitin Gudanarwar APC a jihar.

Ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen mutum, jagora, abun koyi, wanda ya hidimta wa APC da daukacin jama’ar Karamar Hukumar Ukum.

Yaro ya kara da cewa za a sanar da yadda shirye-shiryen yi masa jana’iza za su kasance.