Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Ukum ta Jihar Binuwai, Tony Aboh ya rasu.
Shugaban jam’iyyar a Jihar, Abba Yaro, ya bayyana cewar Aboh ya rasu ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya.
- Kamfanin BUA ya ba UNIMAID tallafin N1bn
- Boko Haram: Attahiru mai fada da cikawa ne —Zulum
- ASUU ta nemi Gwamnati ta magance satar mutane
- Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya da suka mutu a hadarin jiragen sama a tarihi
“Labarin mutuwarsa ya girgiza mu, duba da irin yadda yake da himma wajen hada kan al’umma.
“Muna mika sakon gaisuwa ga iyalansa da daukacin jama’ar Karamar Hukumar Ukum bisa wannan rashi,” a cewar Yaro wanda ya fitar da sanarwar a madadin Kwamitin Gudanarwar APC a jihar.
Ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen mutum, jagora, abun koyi, wanda ya hidimta wa APC da daukacin jama’ar Karamar Hukumar Ukum.
Yaro ya kara da cewa za a sanar da yadda shirye-shiryen yi masa jana’iza za su kasance.