✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Amurka ya sake kamuwa da COVID-19 kwana 4 bayan ya ‘warke’

Tuni dai ya koma ya sake killace kansa

Shugaban Amurka, Joe Biden, zai koma killace kansa bayan ya sake kamuwa da COVID-19, kwana hudu bayan ya warke daga cutar.

Likitan Fadar White House, Kevin O’Connor, shi ne ya tabbatar da haka ranar Asabar.

Ya ce gwajin da aka sake yi wa Shugaban ranar Asabar ne ya tabbatar da sake kamuwar tasa, inda ya ce tuni ya koma killace kan nasa.

“Shugaban dai bai fuskanci wasu alamun cutar ba, kuma yana jin karfi a jikinsa. Sai dai ba dole ne a ci gaba da yi masa magani ba tun da babu dalilin yin haka,” inji likitan.

Shi ma Shugaba Biden ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya ce, “Ya ku jama’a, a yau na sake kamuwa da COVID-19. Hakan dai bai cika faruwa da mutane sosai ba.

“Babu wasu alamun cutar a tare da ni, amma duk da haka zan killace kaina don kare duk wadanda ke kusa da ni. Zan ci gaba da aiki, kuma ina fatan dawowa nan fa wani dan lokaci,” inji Biden

Fadar ta White House dai ta ce tuni Shugaban ya soke tafiye-tafiyen da ya shirya yi zuwa jihohin Delaware da Michigan.

Mai shekara 80 a duniya, Joe Biden, wanda shi ne shugaban Amurka mafi tsufa a tarihi dai lafiyarsa na samun matukar kulawa yadda ya kamata.