✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Amurka ya kamu da COVID-19 duk da an yi masa rigakafinta

Ya kamu da cutar duk da an yi masa rigakafi

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kamu da cutar COVID-19 sakamakon gwajin da aka yi masa, lamarin da ya tilasta masa killace kansa.

Shugaban mai shekara 79 da haihuwa an riga an yi masa dukkan alluran rigakafin biyu na ka’ida ta kariya daga kamuwa daga ita, amma sai ga shi alamun cutar ta bayyana a gare shi.

A wata sanarwa da fadar White House ta fitar ranar Alhamis, ta ce yanzu haka shugaban yana fama ne da ‘wasu  alamu masu sauki’ na cutar ta Kwarona.

Sakamakon haka shugaban zai ci gaba da gudanar da ayyukansa ne a inda ya ke a killace.

A cewar sanarwar, shugaban zai ci gaba da halartar taruka ta hanyar intanet da kuma wayar tarho.

Sanarwar wacce Kakakin Fadar ta White House, Misis Jean – Pierre ta sa hannu, na cewa kamar yadda tsarin aikin fadar ya ke, Joe Biden zai ci gaba da aiki a killace, har sai gwaje-gwajen da aka yi masa sun nuna ba ya dauke da alamun cutar baki daya.

Matar shugaban, Lady Jill Biden wacce ta ke garin Delaware, gwaje-gwaje sun nuna ba ta dauke da cutar, a cewar sanarwar.