✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Amurka ya auna arziki bayan faduwa a keke

Bayan kai masa agajin taya shi mikewa, Joe Biden ya ce garau yake.

Shugaban Amurka Joe Biden, ya auna arziki bayan fadowa daga keke yana tsaka da tuki a kusa da wani gidansa na bakin teku da ke Jihar Delaware a ranar Asabar.

Wani hoton bidiyo da ya karade dandalan sada zumunta ya nuna Shugaban Amurkan mai shekaru 79 ana taya shi mikewa bayan faduwar, yana mai cewa “kalau nake babu abin da ya same ni.”

Bayanai sun ce Shugaban Amurkan ya fita shawagi ne a kan keke tare da matarsa, Jill Biden, a kusa da wani wurin shakatawa da ke makwabtaka da gidansa na bakin teku a Rehoboth.

Tsautsayin dai ya auku ne yayin da Joe Biden din ya yi kokarin tsayawa ya yi magana da masu kallonsa a gefen hanya.

Yadda Shugaban Amurkan Joe Biden ya wada-wada a kasa bayan faduwarsa a keke

Shugaban Amurkan ya shaida wa wadanda suka yi gaggawar kai masa agaji cewa rashin tsayuwa daidai ne ya janyo masa tsautsayin a yayin da yake kokarin zaro kafarsa guda daga fedar keken.

Majiyoyi daga Fadar White House sun bayyana cewa, Shugaban yana cikin koshin lafiya domin kuwa babu kwarzane ko wata buguwa da ya samu, saboda haka ba ya ko bukatar ma’aikatan lafiya su duba shi.

Daga bisani Fadar White House ta wallafa wasu hotunan bidiyo suna nuna Shugaban cikin karsashi domin kore duk wani shakku a kan koshin lafiyarsa.

Bayan halartar hudubar ranar Lahadi a wani coci, manema labarai sun nemi jin ta bakin Shugaban dangane da ko ya samu rauni a sakamakon faduwarsa a keke.

Sai dai Shugaba Biden ya yi buris da tambayar, inda ya dan yi sassarfa ta kusan taku uku a matsayin manuniyar cewa garau yake ba tare da ya cewa manema labaran uffan ba.

Kasancewarsa Shugaba mafi tsufa da aka taba yi a tarihin Amurka, koshin lafiyar Joe Biden ta ci gaba da zama abar jefa ayar tambaya da nuna damuwa a kai, inda har an soma jita-jitar ko zai sake neman wa’adi na biyu a 2024.

A watan Nuwamban 2020, bayan zabensa a matsayin Shugaban Amurka gabanin karbar rantsuwar kama aiki, Biden ya karye a dan yatsansa na kafa a lokacin da yake wasa da wani karensa da ake kira German Shepherds

Sai dai a watan Nuwamban 2021 bayan shekara daya ke nan, likitansa ya tabbatar masa da cewa ya warke garau.