Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump da matarsa Melania sun kamu da cutar COVID-19 wata guda kafin babban zaben kasar da yake neman wa’adin mulki na biyu a ciki.
Trump ya kamu ne bayan wani hadiminsa, Hope Hicks mai shekara 31, ya harbu da cutar, a daidai lokacin da ake muhawara tsakanin ‘yan takarar Shugaban Kasar wadda tsohon mataimakinsa, Joe Biden, ke kalubalantarsa a karkashin inuwar jam’iyyar Demokrat.
“Ni da matata mun kamu da COVID-19 kuma nan take za mu killace kanmu domin fara samun kulawa har mu warke tare”, inji sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma’a 2 ga Oktoba, 2020.
Shugaban mai shekara 74 da ke neman tazarce a zaben Amurka da ke tafe a watan Nuwamba, na daga cikin rukunin mutanen da COVID-19 ta fi yi wa illa.
- Bikin cika shekara sittin: ‘Yan Najeriya sun fadi ra’ayoyinsu
- Jawabin Buhari kan farashin man fetur ya janyo cece-kuce
- An gargadi masu fafutikar kafa kasar Oduduwa
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce masu shekaru sama da 60 da masu fama da cututtuka masu tsanani da masu kusantar masu cutar su ne mafiya hadarin kamuwa da ita.
Jami’an Fadar Whita House sun ce shugaban da maidakin tasa na killace a gida suna samun kulawar likitoci.
A ranar Talata an ga Melania sanye da takunkumi a wurin muhawarar ‘yan takarar shugaban kasa da aka haska a talabijin, a Cleveland, Ohio.
A baya an sha yin maganganu game da rashin ganin shugaban na sanya takunkumin kariyar cutar, kafin daga bisa a daidaikun lokuta aka fara ganinsa yana sanyawa.
Amurka ita ce kasar da ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar a fadin duniya.
A halin yanzu ana kokarin samarwa da kuma wadatar da rigakafin cutar COVID-19 a fadin duniya inda a wasu yankunan aka samu saukinta tare da bude wasu harkokin yau da kullum da taruwar jama’a.
Duk da nasarorin da aka samu wajen yaki da cutar, an samu koma baya a wasu sassan duniya, inda a wasu kasashe da da yankuna ake sake sanya dokar kulle.
A farkon shekarar 2020 ne aka fara samun bullar bakuwar cutar a yankin Wuhan na kasar China, kafin daga bisani ta yadu ta zama annobar duniya.
Bullar cutar ta durkusar da harkokin gwamnatoci da tattalin arziki baya ga dimbin asarar da a aka tafka ta sanadiyyarta.