Shugaban karamar Hukumar Tafa da ke Jihar Neja Alhaji Ado Abubakar ya bayyana shirin koyar da sana’o’in hannu da Kwalejin Young Doctors Academy ke gudanarwa a matsayin makomar ilimi a Najeriya, inda ya bayyana ilimin sana’o’in da cewa shi ne kadai hanyar magance matsalar rashin aiki da ke fuskantar kasar nan.
Shugaban ya bayyana haka ne a wajen Bikin Ranar Jawabi da Rarraba Kyaututtuka ta Kwalejin Young Doctors Academy da ke garin Gauraka a karamar Hukumar Tafa a ranar Asabar din makon jiya.
Kwalejin Young Doctors Academy makaranta ce mai zaman kanta da ke kokarin kirkiro abubuwa inda take sake fasalin ilimi tare da hada shi da hanyoyin samar da aikin yi.
Ya ce, gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen kawo babban sauyi a bangaren ilimi na karamar hukumar. Ya ce sassan da ake gudanar da karamar hukumar ke kawo sauye-sauyen sun hada da horar da malamai kan kimiyyar sadarwa da sanya ido a kan makarantu masu zaman kansu da kara ayyukan manhaja da gyara makarantu da samar da takardun karatu da kuma inganta kwarewar malamai.
Da yake jawabi tsohon Shugaban karamar Hukumar Tafa, Alhaji Ya’u Ahmed ya bayyana rashin kudi da faduwar darajar ilimi da rashin dakunan karatu da magudin jarrabawa da karin girma barkatai a matsayin manyan matsalolin da ilimi ke fuskanta a Najeriya.