A yau Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose suka hadu suka yi musabaha a taron Majalisar tsaro ta kasa karkashin jagorancin Shugaba Buhari a Abuja.
Shi dai Gwamna Fayose mutum ne mai yawan kalubalantar ayyukan da Shugaba Buhari ya yi.
Taron ya samu halartar gwamnoni da tsofaffin shugabannin kasa.