Tun bayan sanarwar da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayar cewa ranar Litinin za a yi bukukuwan Sallah a Najeriya, shirye-shirye sun fara kankama a birane da kauyuka, musamman a Arewacin kasar.
Hakan ya bai wa masu sana’ar hannu musamman teloli, masu kunshi, kitso da sauransu damar dorawa daga inda suka tsaya game da ayyukansu da suka shafi bikin sallar.
A Jihar Kano alal misali, kusan duk inda mutum ya zaga a cikin kwaryar birni da kewaye zai tarar da yadda teloli ke baje-kolin dinkuna don tabbatar da cewar sun faranta wa wadanda suka sabawa alkawari.
Kazalika, idan aka leka gidan lalle ko kunshi, nan ma za a tarar da shi makare da yara mata da manya da ke rubibin ganin cewar sun shiga sahun masu kwalliyar Sallah karama.
Shi ma gida kitso idan ka leka ba a bar shi a baya ba, tuni mata suka ci gaba da yin dandazo don caba adon sallah da za a gudanar a ranar Litinin din.
Su kuwa magidanta, musamman wadanda ba su kammala wa shirin sallar ba a ranar Lahadi, su ma dama ta samu a wajensu, bayan aka tabbatar da cike azumin zuwa 30.
Cinikin kaji ya kankama a Kano
Tuni dai duk inda ka zagaya a cikin Kanon ta Dabo, za ka iske ana gididdiba kaji, naman shanu da sauransu don yin tuwon sallah.
Kasuwanni kuwa abun ba a cewa komai, don kuwa kusan kowace kasuwa da ke Kano da kewaye tana nan ba masaka tsinke.
Kasuwar ’Yankaba, Kantin Kwari, Kasuwar Wambai, Kofar Ruwa, Dawanau, Sabon Gari, Singa da sauransu, abun ba a cewa komai sai wanda ya gani.
Ana ta yanka shanu a Zariya
A birnin Zariya ma da ke Jihar Kaduna maginta na ta kokarin kammala kayan da ya dace ko Allah ya basu ikon saya wa iyalansu domin gudanar da bukukuwan na Sallah Karama.
Ginsami alal misali hadaka ne da magidanta ke yi domin a sayi saniya a yanka a rarraba naman.
Kamar yadda Malam Yusha’u Muhammad ya yi bayani, sun kwashe sama da wata uku suna hada kudi domin irin wannan ranar kuma ga shi Allah ya kawo ta.
Aminiya ta kuma ziyarci masu sayar da kayan miya a Zariyan.
Abdullahi Saudau, wani mai sana’ar kayan mutane ya ce, shi gara ma da aka ce Sallah sai ranar Litinin domin sai Lahadi ne Allah ya ba shi abin da zai yi cefanen Sallah duk da yana ma’aikaci, saboda ya ce ba a yi albashi ba.
Sai dai ya ce cikin rufin asirin Ubangiji, a yanzu ya samu abin cefanen Sallar.