A wannan tattaunawar da aka yi da Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ya bayyana matakan da suka tsara don magance matsalar rashin ingancin sabis a Najeriya
Mene ne shirin Hukumar NCC na kawo karshen rashin ingancin sabis da kamfanonin tarho ke fuskanta?
Akwai karancin kayayyakin da ake bukata a harkar sadarwa wanda hakan babban kalubale ne ga harkar, Najeriya na bukatar karin tashohin na’urar a shiyyoyin kasar, idan aka aiwatar da hakan za a samu sauyi a harkar da kuma bunkasar harkokin tarho. Sauran matsalolin da harkar tarho ke fuskanta sun hada da: datsewar wayoyin da ke haduwa da na’urar da karancin wutar lantarki da sauransu. Hukumar NCC tana da damar bin diddigin ingancin harkokin sadarwa a kasa baki daya. Za mu iya amfani da tsarin binciken karfin na’urar sadarwa ta amfani da’ KPIs’ don gano inda matsalar take tare da tuntubar kamfanin sadarwa da ke da matsalar don ya magance ta, sai dai wasu kamfanonin sadarwa ba su da isassun kayan aiki. Mun riga mun kammala batun yin tara ga kamfanonin sadarwar saboda matsalar ingantaccen sabis, a yanzu haka muna ci gaba da bincike kan matsalar tare da kara musu kwarin gwiwa a kan su kara tanadar kayan aikin da za su iya inganta musu harkokin sadarwarsu.
Rajistar layin SIM ya kasance matsala. Mene ne matakin NCC a kan wannan lamarin?
Bayan kammala rajistar layin SIM muna da bayanan wadanda aka yi wa rajistar. Duk bayanan da aka nada a layin zai kasance wanda ba gamsashshe ba har sai an yi nazari a kansa. Akwai manhajar da take yin nazarin a kan bayanan da aka sanya a layin da aka yi wa rajistar da zarar mun yi amfani da manhajar za ta tabbatar mana bayanan da aka shigar na gaskiya ne ko na karya, idan har babu gaskiya a cikin bayanan layin SIM sai a rufe layin don mayar wa wanda ya yi rajistar don sake wata rajistar da aka tsara. Rajistar layin SIM na daya daga cikin matakan tsaron kasa, ya zama wajibi mu gabatar da shi. Ya zama wajibi ’yan Najeriya su dakatar da sayar da layukan tarho masu rajista saboda yin haka saba doka ne kuma yana ja wa kasar barazanar tsaro.
Kwanaki Hukumar Tara Haraji ta Najeriya (FIRS), ta kai karar cewa, kamfanonin tarho ba sa shigar da kudin harajin bAT ga gwamnati hakan yana kawo wa kasar koma-baya. Wene mataki NCC ke dauka a kan haka?
Mun kasance masu kiyaye doka, don haka muna bukatar duk masu kamfanonin sadarwa su kasance masu kiyaye doka kuma su biya duk harajin da za su biya a kan lokacin da ake bukata. A kan wannan batun muna shawartar masu kamfanonin sadarwa su biya bashin kudin harajin da ake biya a kan kayan da mutane suke saye yau da kullum (bAT) da sauran haraji da ya dace su biya gwamnati. Muna kara nanata wa Hukumar FIRS ta sanya tara ga wadanda suka ki biyan kudin haraji. Hukumar FIRS dokar kasa ce ta kafa ta, ba za mu iya shiga cikin hurumin aikinta ba. Don haka ya zama wajibi kamfanonin sadarwa su biya kudin haraji kamar yadda doka ta tanada.
Har yanzu manyan kamfanonin sadarwa na fuskantar barazanar kiran waya ta bogi. Ta yaya NCC za ta iya magance wannan?
Kiran waya da ake yi ga abokan hulda da nufin yaudara ko damfara, abu ne da Hukumar NCC ke bakin kokarinta, ba kawai ya saba wa doka ba ne, yana kawo wa kasar nan barazana a harkar tsaro. Mun gano wasu kamfanonin sadarwa da suka yi sake ana amfani da na’urarsu sannan, mun ci tarar su, a yanzu haka muna ci gaba da binciken karin wasu kamfanonin a asirce. Rahoton kididdiga na nuna adadin masu kiraye-kirayen yayin da masu kiran suke boye lambarsu da bayanansu da gangan wannan yana kawo koma-baya, ba za mu taba gazawa ba har sai mun dakile masu aiwatar da wadannan ayyuka. Mun kaddamar da na’urar da take tantance irin wannan kiran wayar bogi ta amfani da ‘SIM Bodes’, wadda karamar na’ura ce da za ta iya amsa kira ta watsa bayanan da ya shigo mata. Na’urar karama ce kuma zata iya tantance kasuwancin karya da wadanda suke yin harkar, yayin da za a iya amfani da na’urar a ko’ina a sassan kasar nan. Kamata ya yi a ce duk wani fitar kiran wayar sadarwa sai ya biyo ta tace bayanai (BTS) amma wasu batagari sukan tsallake su fara na’urar tafi da gidanka don bukatun kansu.
Duk da kalubalen da ke bayyane, muna bukatar fasahar da za ta magance matsalar tare da bayyana masu aikata harkar da kuma dakatar da kiransu a kasar nan. Mun riga mun gano mutanen da ke aikata irin wadannan kiran wayar bogin saboda tsadar farashin da dakatar kiran waya daga kasashen duniya da na gida. Amma dakatar da kiran na cikin kasar nan ya fi sauki, don haka suka yanke shawarar boye lambarsu da bayanansu daga wasu kasashe, amma akwai masu yin kiran waya a cikin kasa sai su boye lambarsu maimakon su biya kudin dakatarwa mai yawa.
Mun fahimci akwai jinkiri da aka samu bayan kammala sayar da Kamfanin 9mobile, da mika ragamar kamfanin ga wadanda suka saya. Me za ka ce game da wannan jinkiri?
Jinkirin da aka samu bayan kammala sayar da Kamfanin Sadarwa na 9mobile da mika ragamar kamfanin ga kamfanin Teleology Holdings Limited wanda ya saya, hakan zai yiwu akwai abin da ya janyo jinkirin. Da farko akwai yawan bashin da ake bin Kamfanin 9mobile wanda sai an warware komai kafin sabon kamfanin da ya saya ya karbi takardun kamfanin. Hukumar NCC na bin Kamfanin 9mobile sama da Naira biliyan 15 kudin harajin shekara da wasu kudade da ya kamata su biya, wanda hakan yana daga cikin tsarin da hukumar ta tanada ga duk wani kamfanin sadarwa da zai sayar da kamfani sai an yi bincike. Kamfanin 9mobile da farko ya rubuta wa NCC takarda a kan tambayar zai iya sanya hannun jarinsa a kasuwa ga kamfanonin sadarwa, wanda a lokacin 9mobile yana kasuwa, zuwa manajan United Capital Trustees kuma wakilin bankuna 13 da suka bai wa Kamfanin Etisalat rancen kudi wanda a yanzu suka canja wa kamfanin suna zuwa 9mobile. Hukumar NCC na bin Kamfanin 9mobile Naira biliyan 12 kudin AOL na shekarar 2016 da 2017 Naira biliyan daya na adadin biyan kudin shekara biyu da kuma Naira biliyan 2.3 na kudin na’urar sadarwa. Sai dai a yanzu Kamfanin 9mobile ya biya kashi 50 cikin 100 na adadin Naira biliyan 15 da NCC ke bin su, yayin da NCC ta rubuta wa kamfanin wasika a kan ba matsala na bukatun da suka gabatar da kuma bayar da hannun jarinsu ga EMTS zuwa United Capital, kamar yadda 9mobile ya bukata.
Sannan akwai wata bukatar da 9mobile ke so ga NCC akan amincewarta na mika hannun jarinsu ga hannun United Capital zuwa ga Teleology, mun ba su sharadi kafin mu amince da bukatarsu. Sharadin shi ne sai 9mobile ya nuna wa NCC alamar rajistar Kamfanin Teleology da ya yi da Hukumar yi wa Kamfanoni Rajista (CAC) da sharadin tsare-tsaren da aka gindaya wa kamfanin Teleology daga Hukumar NCC don tabbattar da cewa Kamfanin 9mobile yana da fasahar sadarwar gudanar da harkokin sadarwa. An kaddamar da kwamiti wanda zai binciki karfin gudanar harkokin kamfanin sadarwa na Teleology. Da zarar sun cika sharuddan da ake bukata, sai mu tura musu sakon amincewa ta karshe da wasikar kin amincewa na fitar da hannun jarinsu daga United Capital zuwa Teleology. Za a sanar da sakamakon binciken rahoton Teleology kuma muna hanyar kammala sayar da Kamfani 9mobile, za mu tabbatar wa ’yan Najeriya cewa mun kammala idan har an cika sharuddan.
Akwai batun da ke da alaka da irin wannan, lokacin da MTN ya sayi bisafone a watan Janairu 2016 daga bisani bisafone suka bukaci a maida wa MTN lasisinsu 800MHz. yaya aka kare, mene ne matsayin NCC a kan mayar da lasisin kamfanin?
Sama da shekara ke nan Kamfanin bisafone ya bukaci NCC ta bai wa MTN lasisinsa sakamakon kadarorin da bisafone zai bai wa MTN a shekarar 2015. Sun tambayi kashi 100 cikin 100 na hannun jari daga Kamfanin bisafone zuwa MTN, sannan mun amince da bukatunsu bayan cika sharuddanmu.
Daga bisani, an samu rahoton cewa Kamfanin bisafon bai nemi a mayar wa MTN lasisin kamfanin ba, mika ragamar lasisin kamfani ba abu ne da ake yi kai-tsaye ba, saboda akwai abubuwan da sai an gabatar da su. Mun fada musu cewa, an kaddamar da Hukumar NCC karkashin dokar kasa yayin da muka gayyaci masu ruwa-da-tsaki da suka hada da kafafen sadarwa don ganawa da su. Sakamakon ganawar da aka yi zai tabbatar da amincewarsu a bukatar da suka nuna ta biyu. Mun riga mun kammala rahoton ganawar da aka yi, a yanzu haka muna jiran martani daga wadanda abin ya shafa don bayar da bahasi. Har sai mun hada martanin masu ruwa-da-tsaki kafin mu bayar da damar amincewa ko rashin amincewa.