✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin Allah domin fansar dan Adam (4)

A rana Juma’ar da ta gabata ne dukan Kirista a duniya suka tuna da shigowar Yesu Kiristi cikin wannan duniya tamu mai mugunta kuma mai…

A rana Juma’ar da ta gabata ne dukan Kirista a duniya suka tuna da shigowar Yesu Kiristi cikin wannan duniya tamu mai mugunta kuma mai cike da zunubi domin abu guda daya kawai – wato Fansar Mutum daga bautar Shaidan da kuma zunubi. Tun daga farkon farawa dai bayan da Allah Madaukakin Sarki Ya halici mutum, Ya kuma sa shi aikin gonar Adnin wanda shi Allah da kanSa Ya dasa; mutum yana tafiya daidai yadda ya kamata har zuwa lokacin da Shaidan ya rudi Adamu da Hauwa’u. Dukan mu ’yan Adam zuriyarsu ne; da yake su ne mutane na farko da Allah Ya halita, Ya kuma ba su iko su hayayyafa su mamaye dukan duniya, wannan kuwa tun kafin su yi zunubi ne; suna dauke ne da dukanmu a mararsu. Allah Ya ba su ikon yawaita su kuma hayayyafa su cika dukan duniya kamar yadda Ya alkawarta masu a cikin Littafin Farawa 1: 26 – 28, “Kuma Allah Ya ce, bari Mu yi mutum a cikin surarmu, bisa ga kamanninmu, su yi mulki kuma bisa kifaye na teku da tsuntsaye na sama, da bisashe da kuma bisa dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe wanda ke rarrafe a bisa kasa. Allah fa Ya halita mutum cikin sura tasa,cikin surar Allah Ya halice su. Allah Ya albarkace su kuma, Allah Ya ce masu, ku yalwata da ’ya’ya, ku ribu, ku mamaye duniya, ku mallake ta; ku yi mulkin kifaye na teku da tsuntsaye na sarari da kowane abu mai rai wanda ke rarrafe a kasa.” Duk wannan alkawari da albarkoki masu girma Allah Ya yi wa Adamu da Hauwa’u ne kafin su yi zunubi. Abin kaito kuwa shi ne, kafin su haifi dansu na farko, sun rigaya sun aikata zunubi, domin wannan ne kowa da suka haifa tun daga wancan lokacin; ya zama mai dauke da zunubi ne domin ainihi a cikinsu muke. Misali, idan kana da bishiyar mangoro da soma ba da ’ya’ya, da ka taba sai ka ji wannan mangoron ba zaki ko kadan sai dan karen tsami; idan ka dauki ’ya’yan wannan mangoro ka je ka shuka su a wani wuri; shin zai ba ka mangoro mai zaki ne? Babu ko kadan; mai tsamin ne zai ba ka har sai wannan bishiyar mangoron ta mutu domin haka ne duk irin da ke cikin wannan bishiyar, ba za ta iya haifar da wasu irin ’ya’ya ba sai mai tsamin kawai a koyaushe. Ba za ka iya canja irin wannan ba, sai dai ka samo canjin iri na mangoro mai zaki. Haka yake da yake Adamu da Hauwa’u ne iyayen dukan ’yan Adam, babu yadda za a samu bambanci tsakanin mu ’ya’yansu da su kansu da yake sun yi zunubi, haka dukanmu; mun zama masu zunubi domin daga cikinsu muka fito.
Yadda muka rasa ’yancinmu:
A cikin tarihin halitta wanda Allah Ya yi bisa ga Littafi Mai tsarki, maganar Allah na koya mana cewa: “Ubangiji Allah kuwa Ya sifanta mutum daga turbayar kasa, Ya hura masa numfashin rai cikin hancinsa, mutum kuma ya zama rayayyen mai rai. Ubangiji Allah kuma Ya dasa gona daga wajen gabas, a cikin Adnin, can kuwa ya sanya mutumin da ya sifanta. Kowane itace da ke mai sha’awar gani, masu kyau kuwa domin ci, Ubangiji Allah Ya sa ya tsiro daga kasa; itacen rai kuma a tsakiyar gona, da itacen sanin nagarta da mugunta…….sai Ubangiji Allah Ya dauki mutum Ya sanya shi cikin gonar Adnin domin ya aikace ta, ya tsare ta kuma. Ubangiji Allah kuma Ya dokaci mutumin, Yana cewa, an yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sake: amma daga cikin itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka diba ka ci ba: cikin ranar da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” (Farawa: 2: 7 – 9, 15 – 17). Wannan shi ne umarnin da Allah Ya ba wa shi mutum. Abu guda daya ne kawai Allah Yake so da shi mutum – BIYAYYA. Idan da mutum ya ci gaba da yin biyayya da umarnin Allah, da babu zunubi a cikin wannan duniya, amma Shaidan ba ya son wannan ya faru, shi ya sa ya rudi mutum ya yi wa Allah rashin biyayya. Allah bai boye wa mutum hukuncin aikata zunubi ba tun daga farko; Ya riga Ya gaya masa cewa cikin ranar da ka ci, mutuwa za ka yi lallai: har a yau wannan shari’a ba ta canja ba – hakkin zunubi mutuwa ne. A cikin Farawa 3: 1 – 7: “Amma maciji ya fi kowane dabbar da Ubangiji Allah Ya yi hila. Ya fa ce wa macen, ashe, ko Allah Ya ce, ba za ku ci daga wannan itatuwa na gona ba? Sai macen ta ce wa macijin, daga ’ya’ya na itatuwan gona, an yarda mana mu ci: amma daga ’ya’yan itace wanda ke cikin tsakiyar gona, Allah Ya ce ba za ku ci ba, ba kuwa za ku taba ba domin kada ku mutu. Sai macijin ya ce wa macen, ba lallai ne za ku mutu ba: gama Allah Ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su bude, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta. Sa’adda macen ta lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin ba da hikima, sai ta debi ’ya’yansa, ta ci, ta kuma ba mijinta tare da ita, shi kuwa ya ci. Dukansu biyu kuwa idanunsu suka bude, suka waye kuma tsirara ne su; suka dundunke ganyayen baure, suka yi wa kansu mukuru.”
Yadda zunubi ya shigo duniya ke nan. Tun daga wancan lokaci Allah Ya soma tunanin yadda zai ceci mutum daga bautar zunubi.  Tun daga zamanin Annabawa; Allah Ya soma shirya hanyar da zai fanshi mutum daga bautar zunubi. Hadaya ita ce kawai hanyar fansa daga cikin bautar zunubi; shi Ya sa Allah Ya umurci Annabi Ibrahim ya je kan duwatsun Moriah ya mika dansa na alkawari wato Ishaku wanda matarsa Saratu ta haifa masa, hadaya ta konawa, da ya je bisa wannan dutsen kuwa, sai ya daure wannan yaro ya sa shi bisa bagadi , ya dauki wuka zai sa ke nan a wuyan wannan yaron nasa Ishaku, sai Allah Ya kira shi ya ce, yanzu na sani kana sona, kada ka yi rauni wa wannan yaron , ka dubi bayanka; za ka ga rago cikin sarkakiya, ka yanka domin hadaya a madadin danka, haka Ibrahim ya yi. Za mu duba idan Allah Ya bar mu cikin masu rai mako na gaba yadda dukan wannan ya nuna mu ne ga zuwan Yesu Kiristi ciki duniya domin ya fanshe daga bautar zunubi. Abu guda wanda ina so mu sani shi ne – a kan duwatsun Moriah ne aka gicciye Yesu Kiristi, shi wanda shi ne dan Rago Na Allah. Mutuwar Yesu Kiristi da tashinsa daga matattu shi ne sanadin ceton da muke da shi. Haka nan ga dukan wanda ya ba da gaskiya da wannan shiri na Allah domin fansar dukan ’yan Adam. Ubangiji Ya sake fahimtar da mu domin mu sami wannan ceto sauwake, amin.