Ministan Hajji da Umara na kasar Saudiyya, Dakta Muhammed Saleh Benten, ya ce shirin da aikin Hajji na bana ba a taba yin irinsa ba ta yadda zai saukaka wa alhazai yi ibadar cikin nutsuwa.
A yayin da yake ziyarar duba aikace-aikace da tsare-tsare na Hajjin bana, Benten ya ce, “Hukumomin tsaro, lafiya da ayyuka ne za su aiwatar da gagarumin shirin da a ka tanada.
“Tsare-tsaren sun hadar da samar da kiwon lafiya da ba a taba samun irinsa ba.
“Akwai kuma ganagriyan tsarin lura da cunkoso da za a aiwatar da shi a kan bin ka’idojin kariya daga yaduwar cututtuka wanda Hukumar lafiya ce ta samar da shi domin kare alhazai daga kamuwa da annoba”, inji shi.
Benten ya kuma jinjina wa kokarin da Sarki Salman da dansa Yarima Mohammed Bin Salman wajen lura da aikin Hajjin bana ta hanyar duba matakan kariya domin tsare alhazai daga kamuwa da dukkan nau’in cututtuka.
Kafin nan, Ministan ya yi rangadin duba tsaren-tsaren tarba da makwancin alhazai a birnin Makkah.
Ma’aikatan hukumar sun yi masa bayanai a kan tasrin da a ka yi na tarba da masaukan da alhazai da za su zauna daga ranar 4 zuwa 8 ga Dhul Hijja kafin su tafi Mina.
Sannan Benten ya ziyarci tantunan alhazai a Arafat da kuma kayan aikin da ke Muzdalifah, inda alhazai za su kwana bayan tsayuwar Arfah.
Ya kuma kai ziyarar duba aiki zuwa birnin tantuna na Mina inda ya nuna gamsuwa da irin tsari da kayan aikin da a ka tanada, musamman bangaren makwanci da abincin alhazai.
A karshen ziyarar, Ministan ya kalli majigi na tsare-tsaren aikace-aikace da a ka tanada domin alhazai lokacin tafiyar da za su yi daga makwantan su zuwa Jamrat domin yin jifa