Idan ba mu manta ba, makon jiya mun tsaya ne a kan wannan magana cewa, masu bin Yesu Kiristi su ne aka kwatanta da Gishiri da Haske a cikin wannan duniya. Mun ga yadda dole rayuwar kowane mai bin Yesu Kiristi ta kawo dandano ga rayuwar sauran mutane da ke kewaye da shi. Haka nan kuma; dole ne rayuwarsa ta nuna haske ta wurin kyawawan ayyukansa da sauran jama’a za su iya gani su kuma girmama sunan Allah. Muka gani cewa; idan hasken mai bi tana haskakawa, abin da mutane za su gani shi ne – kyawawan ayyukansa.
A yau bisa ga yardar Ubangiji Allah, za mu ci gaba da yin bincike game da shirin da ya kamata mai bi ya yi kafin fyaucewa. Bari mu sake yin karatu daga cikin maganar Allah a Littafin 1Korinthiyawa 3 : 6 – 15 wadda take cewa “Ni na dasa, Appollos ya yi ban ruwa, amma Allah ne Ya ba da amfani. Domin wannan fa shi wanda ya dasa ba komai ba ne, ko shi wanda ya yi ban ruwa kuma; sai Allah Wanda ke ba da amfani. Yanzu fa, da mai dashe da mai ban ruwa daya ne; amma kowane za ya samu nasa lada gwargwadon wahala tasa. Gama mu abokan aiki na Allah ne, ku kuma gonar Allah ne, ginin Allah ne. Ni kuwa, bisa ga alherin Allah da aka ba ni, kamar magini mai gwaninta na kafa gindi, wani kuwa yana ta da gini a kai, amma sai kowane mutum ya yi hankali irin ginin da yake yi a kai. Gama ba wanda yake da iko ya kafa wani gindi daban da wanda an rigaya an kafa, Yesu Kiristi ke nan. Amma idan kowane mutum ya yi gini bisa gindin nan, ko zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ingirci, ko tattaka, aikin kowane mutum za ya bayyana: gama ranar nan za a tone shi da yake cikin wuta za a gwada ta; wuta kuwa da kanta za ta gwada aikin kowane mutum kowane iri ne. Idan aikin kowa da ya gina a kai ya tsaya, za ya karbi lada; idan aikin kowa ya kone, za ya sha asara, amma shi da kansa za ya tsira; amma sai ka ce ta wurin tsakiyar wuta.”
Wane irin shiri ne ya kamata mai bi ya yi kafin zuwan Yesu Kiristi? Ina so ne mu lura da inda muka yi karatu, ashe kowane abin da muke yi a matsayinmu na masu bi – GINI NE; wannan ba wai aikin da muke yi cikin ekklisiyya kadai ba ne, a’a, amma dukan abin da muke yi cikin rayuwarmu ta yau da kullum; ko a makaranta, ko a kasuwa, ko a gida, ko a kanti ko a ko’ina ma; mu lura, duk abin da muke yi an kwatanta shi da yin gini. Idan mun aikata alheri – gini muke yi; idan mun aikata mugunta – gini muke yi. A rayuwar yau da kullum mukan ga kayan gini iri-iri; wadansu da jalap – wato birkin kasa/laka; wadansu kuwa da bulo bugun inji, har ila yau akwai wadansu kuma da duwatsu suke nasu ginin; akwai wadansu kuwa da katakai suke yin nasu, wannan gini ne na wannan duniya.
Maganar Allah tana cewa, za mu iya rayuwa mai kyau a gaban Allah har a iya kwatanta shi da zinariya domin kyaunsa, ko azurfa, ko kuwa duwatsu masu daraja. Akwai kuma wadansu wadanda suka yi amfani da itace suka yi nasu ginin; wadansu kuwa da ciyawa, ko tattaka; abin lura shi ne, duk aikin da kowane mutum mai bin Yesu Kiristi ya yi, sai Allah Ya gwada aikin Ya ga kowane irin aiki ne shi. Kuma zai gwada ne da wuta. Idan har wutar nan ta kone aikin; to ka rasa naka ladan ke nan, ma’ana shi ne ba ka yi wancan aiki bisa ga ka’idar Allah ba. Za ka sha asara sosai. Mun san cewa komai kyaun gini, idan na kara ne ko itace, sai aka kawo wuta wurin domin a gwada ingancin wannan gini, mu san lallai wannan gini ba zai jure wa harshen wuta ba, zai kone kurmus ya zama toka.
Tambayar da ta zama dole sai mun amsa ita ce – Mece ce wannan wuta da Allah zai yi amfani da ita domin gwada ayyukan da muka yi a cikin duniya? Kafin mu amsa wannan tambaya; bari mu yi karatu daga cikin Littafi Mai tsarki: Irmiya 23: 29 tana cewa; “Maganarka ba kamar wuta take ba? Kamar guduma mai farfasa duwatsu?” ’Yan uwana bari mu yi lura sosai da wadannan kalmomin da mun karanta yanzu – A nan mun gane cewa Magarnar Allah kamar wuta ce. To; ashe lokacin shari’a, abu guda da Allah zai yi amfani da shi domin shar’anta masu binSa, shi ne maganarSa. Manufar wannan kuwa ita ce, Allah Ya riga ya bayana mana nufinSa cikin maganarSa, Allah Ya riga Ya furta nufinSa ga dan Adam cikin kalmarSa, lokacin da zai yi shari’a kuwa, abu guda da zai yi amfani da shi, shi ne MAGANARSA. Dukan abin da mai bin Yesu Kiristi ya yi wanda ba bisa ka’idar maganar Allah ba, zai zama aikin banza ne kawai.
Aiki ne mara amfani, komai kyaun aikin. Allah Ya san tunaninka yayin da kake yin abin da kake yi. Dole ne mu san ko me Allah Yake so mu yi a koyaushe, mu kuma aikata shi. Wutar maganar Allah ne za ta auna aikinmu duka, eh har da irin dalilin/dalilan da ya sa muke yin irin aikin da muke yi. A cikin Littafin Ibraniyawa 4 : 12 – 13 maganar Allah ta ce: “Gama maganar Allah mai rai ce, mai aikatawa, ta fi kowane takobi mai kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa mararrabar rai da ruhu da gababuwa da bargo kuma. Tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta. Babu wani abu mai rai kuma da ba a bayyane a gabanSa ba, amma abubuwa duka a tsiraice suke, budaddu kuma gaban idanun wannan Wanda muke gare Shi.”
Mu lura da wannan, sanin cewa maganar Allah tana da rai, ya kamata mu yi tafiya da ta cancanci kiranmu na masu bi. Rashin sanin maganar Allah, ba zai zama hujja ba a gaban Allah a wancan rana; domin haka, shirin da za ka iya yi yau shi ne – ka san ko mene ne Allah Yake so ka yi a cikin rayuwarka cikin wannan duniya. Ka tuna fa, Yesu Kiristi ya ce ba dukan wanda yake ce mini Ubangiji Ubangiji ne zai samu ceto ko zai tsira ba, sai shi wanda ke aikata nufin Allah; nufin Allah kuwa a bayyane yake cikin maganarSa. Bari mu roki Ubangiji Allah Ya taimake mu mu iya yin tafiyar da za ta gamshe Shi. Amin .
Shiri domin gamuwa da Allah (8)
Idan ba mu manta ba, makon jiya mun tsaya ne a kan wannan magana cewa, masu bin Yesu Kiristi su ne aka kwatanta da Gishiri…