✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shiri domin gamuwa da Allah (5)

Yau kuma Allah ya sake barinmu cikin masu rai, domin mu iya bauta masa cikin ruhu da kuma gaskiya. Wannan alherinsa ne kawai; sai mu…

Yau kuma Allah ya sake barinmu cikin masu rai, domin mu iya bauta masa cikin ruhu da kuma gaskiya. Wannan alherinsa ne kawai; sai mu yi maSa godiya. Idan muka tuna, makon da jiya, mun dan duba wani abu kan muhimmancin samun sunanka a cikin Littafin rai, domin idan ba a iske sunanka ba, babu shakka ba ka da wuri a inda Allah Yake; kuma mu tuna babu matsakaicin wuri a can, ko kana tare da Allah Madaukakin Sarki da mala’ikunSa, ko kuwa kana tare da Shaidan cikin korama ta wuta da aljanunsa. Zabi ya rage a gare mu ne; shi Ubangiji Allah ba Ya tilasta wa kowa ya yi wani abu, koda yake yana da damar yin kowane abin da Ya ga dama a koyaushe kuma. A yau ina so ne mu sake dawowa cikin ainihin koyarwar da muke yi.
Ba dukan mutane na wannan duniya ne za su bayyana a gaban babban farin Kursiyyi na shari’a ba, Allah Ya shirya tun daga farko a kan yadda zai yi shari’arSa. Shari’a ta farko ita ce shari’a wadda za a yi wa masu bin Yesu Kiristi:
Shari’a ta masu bin Yesu Kiristi:
A cikin Littafin 2Korinthiyawa 5 : 10, maganar Allah na cewa, “Gama dole dukanmu za mu bayyana a gaban Dakalin shari’a na Kiristi; dokin kowane daya ya karbi sakamakon aikin da ya yi cikin karfin jiki nagari ko mugu.”  Ina so mu gane wani karamin bambamci da abin da Ruhun Allah yake cewa cikin Ruya ta Yohanna 20 : 11; maganar Allah a nan na cewa; “Na ga kuma babban farin Kursiyyi da wanda ke zaune a bisansa, wanda duniya da sama suka guje wa fuskatasa; ba a kuwa samu masu wuri ba.” Akwai Dakalin Shari’a na Kiristi; akwai kuma babban farin Kursiyyi: za mu so mu yi gajeren bayani kadan a kan Dakalin shari’a ta Yesu Kiristi. idan mun tuna, kwanakin baya mun yi magana a kan fyaucewa na masu bi. A cikin Littafin 1Tassalukawa 4 : 13 -17; maganar Allah na cewa “Amma ba mu son ku da jahilci, ’yan uwa, ga zancen wadanda sun yi barci, kada ku yi bakin ciki, kamar sauran mutane, wadanda ba su da bege. Gama idan mun ba da gaskiya Yesu ya mutu ya tashi kuma, haka nan wadanda sun yi barci cikin Kiristi Allah za Ya kawo su tare da shi. Gama wannan muna fada muku bisa ga maganar Ubangiji, mu da muke da rai, wanzazzu ne har zuwan Ubangiji, ba za mu rigaya wadanda sun yi barci ba ko kadan. Gama Ubangiji da kansa za ya sauko daga sama, da kira mai karfi, da muryar Sarkin mala’iku, da kahon Allah kuma: matattun da ke cikin Kiristi za su fara tashi: sa’annan mu da muke da rai, mun wanzu, tare da su za a fyauce mu zuwa cikin giza-gizai, mu tarbi Ubangiji a sararin sama: haka nan za mu zauna har abada tare da Ubangiji.” A lokacin da aka fyauce masu bin Yesu Kiristi daga cikin wannan duniya, duniya ba za ta kare ba, tukuna amma za a shiga lokacin tsanani na shekara bakwai bisa ga Littafi Mai tsarki. Za mu yi bincike musamman a kan wannan zamani na tsanani wanda zai zo kan dukan wanda ba a fyauce shi ko ita ba. Lokacin wahala kwarai da gaske, eh har da dukan wadanda ba su rike Yesu Kiristi da gaske ba suna wasa kawai da sunan Yesu Kiristi, a lokacin idanunsu za su bude, amma sai da na sani ne kawai za su yi ta yi, domin lokacin da Yesu Kiristi ya zo; ba a shirye suke ba. Dukan wadanda ba a shirye suke ba a cikin zuciyarsu, ba za a fyauce su ba. dukan wadanda ba su da dangantaka da Yesu Kiristi, ba za su ma ji muryar komai ba, domin zuwan Yesu Kiristi domin Ekklesiyarsa ne kawai a wannan lokaci; su kadai za su ji muryar kahon Allah, abin da duniya za ta gani kawai, shi ne, za ta iske cewa akwai wadansu mutane cikin duniya wadanda suka bace kawai kuma babu wani bayani. A lokaci kamar wancan ne kungiyoyi kamar Majalisar dinkin Duniya za su so su hada kan duniya duka wuri daya su kuma samu shugaba daya wanda zai yi mulki, amma mu sani masu bin Yesu Kiristi na gakiya sun rigaya sun tafi tare da shi cikin sama duka da wadanda suka rigaya suka mutu cikin ban-gaskiya. Tambayar da nake so in yi maka ita ce, kana gani idan Yesu Kiristi ya zo yau za ka samu ka tafi tare da sauran masu bi ko kuwa za a bar ka a baya? Dukan wadanda sun ba da gaskiya a cikin Yesu Kiristi za a fyauce su, maganar Allah a cikin Littafin Yohanna 3: 18 na koya mana cewa “Wanda yana ba da gaskiya gare shi ba a yi masa shari’a ba: wanda ba ya ba da gaskiya ba an rigaya an an yi masa shari’a domin ba ya ba da gaskiya ga sunan da haifaffe kadai na Allah ba.”
Shari’ar masu bin Yesu Kiristi daya wato shari’a ta karbar lada bisa ga irin ayyukan da muka yi lokacin da muke raye a cikin wannan duniya. A cikin Littafin 1Korinthiyawa 3 : 9 – 15; maganar Allah na cewa “Gama mu abokan aiki na Allah ne; ku kuwa gonar Allah ne, ginin Allah ne. Ni kuwa, bisa ga alherin Allah da aka ba ni; kamar magini mai gwaninta na kafa gindi, wani kuwa yana tada gini a kai, amma sai kowane mutum ya yi hankali da irin ginin da yake yi a kai. Gama ba wanda yake da iko ya kafa wani gindi daban da wanda an rigaya an kafa ba, Yesu Kiristi ke nan. Amma idan kowane mutum ya yi gini bisa gindin nan, ko zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ingirci, ko tattaka; aikin kowane mutum za ya bayyana; gama ranar nan za a tone shi, da yake cikin wuta ake gwada su; wuta kuwa da kanta za ta gwada aikin kowane mutum na kowane iri  ne. Idan aikin kowa da ya gina a kai ya tsaya, za ya karbi lada; idan aikin kowa ya kone, za ya sha hasara: amma shi da kansa za ya tsira; amma sai ka ce ta wurin tsakiyar wuta.”
’Yan uwana, mu sani fa, cewa duk abin da muke yi a yau, yana nan kamar gini muke yi, dukkan ayyukan da muke yi cikin haikalin Ubangiji, suna nan kamar gini ne, kuma akwai kayan ginin daban-daban, wani da zinariya ne, wani kuwa azurfa ne, wani itace ne, wani kuwa ciyawa ne kawai. Amma a lokacin shari’a, wuta ce za ta gwada kowane aikin da muka yi.
Idan Allah Ya yarda za mu ci gaba daga wannan wuri mu san ko mene ne ainihin manufar wannan wuta da za ta gwada dukan ayyukanmu. Ubangiji Allah Ya taimake mu mu yi aiki wanda zai dauwama. Mu kuma ci gaba da yin addu’a domin kasarmu da wadanda ke shugabanci, musamman Shugaban kasa Muhammadu Buhari; mu roki Allah Ya ba shi lafiya da karfin jiki domin ya aikata nufin Allah a matsayinsa na shugaba. Allah Ya tsare mu duka, amin