✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shiri domin gamuwa da Allah (3)

A yau, bisa ga yardar Ubangiji Allah, za mu ci gaba ne da koyarwar da muka soma makon da ya shige, za mu kuma soma…

A yau, bisa ga yardar Ubangiji Allah, za mu ci gaba ne da koyarwar da muka soma makon da ya shige, za mu kuma soma da masu Bin Yesu Kiristi wato Krista ke nan. Mu masu bi, mu sani cewa da mu ne Allah zai soma wannan shari’a, a yanzu sai mu sani muna sauraron dawowar Yesu Kiristi Ubangijinmu domin ya kai mu wurinSa. Akwai kalma guda wadda duk mai bada gaskiya ya sani kuma ita yake jira FYAUCEWA. A cikin Littafin 1 Tassalunikawa 4:16 – 17, maganar Allah tana koya ana cewa: “Gama Ubangiji da kansa za ya sauko daga sama, da kira mai karfi, da muryar Sarkin Mala’iku, da kahon Allah kuma, matattun da ke cikin Kiristi za su fara tashi, sa’annan mu da muke da rai, mun wanzu, tare da su za a fyauce mu zuwa cikin giza-gizai, mu tarbi Ubangiji a sararin sama: haka nan za mu zauna har abada tare da shi.”

Dukan alamun da Yesu Kiristi ya fadi za su bayyana kafin dawowarsa sun riga sun bayyana, abin da ya rage kawai shi ne dawowarsa; idan har mun iya sanin cewa wannan duniya gaba daya babu wani sauran lokaci, za ta kare haka nan mu kuma ba za mu dauwama a cikinta ba; dole ne ga mai hankali ya yi tunanin gamuwa da mahaliccinsa. Saduwa da Ubangiji Allah dole ne, babu wanda zai iya gujewa a wancan ranar. Koyaushe wannan fyaucewa kan iya aukuwa ko mun yi shiri ko ba mu yi shiri ba, kamar ranar mutuwarka ne, mutuwa ba ta sallama, ranar da ta zo shi ke nan; tafiya za ka yi; shi ya sa dole, a yayin da muke rayuwa, sai mu zauna da shiri domin mutuwa za ta iya kwankwasa kofa, kuma ba ka da ikon hana ta shigowa. Haka nan kuma yadda zuwan Yesu Kiristi zai kasance, a daidai lokacin da ba ka yi tsammani ba zai zo ya fyauce masu bin sa. Maganar Allah na cewa cikin littafin 1Tassalunikawa 5:2: “Gama ku da kanku kun sani sarai ranar Ubangiji tana zuwa misalin barawo da dare. Suna cikin fadin, kwanciyar rai da lafiya, sai ga hallaka farat ta auko musu, kamar yadda faya ta kan auko wa mace mai ciki. Ba kuwa za su tsira ba ko kadan. Amma ku ’yan uwa, ba cikin duhu kuke ba, da ranar za ta tarshe ku kamar barawo:”
barawo ba ya zuwa gidanka da sallama, ba zai tambayi ra’ayinka ba kafin ya zo, zai zo ne a lokacin da ya ga dama. Idan kuwa haka ne zuwan Yesu zai kasance, wace irin rayuwa ce ya kamata ka yi? Da shi ke ka san cewa dole ne ka bayyana a gaban Ubangiji Allah domin shari’a, kuma babu wani alkali wanda zai tsaya domin ya kare ka; daga kai sai Allahnka. Kuma Shi ne Mai shari’ar. Yesu ya rigaya ya sanar da mu game da ire-iren abubuwan da za su faru kafin ya zo, kuma mun gan su muna kuma kan kara ganinsu. A cikin littafin 2Timothawus 3 : 1 – 7, maganar Allah na koya mana cewa: “Amma sai ku san wannan, cikin kwanaki na karshe miyagun zamuna za su zo, Gama mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, masu ruba, masu girman kai, masu zagi, marasa bin iyaye, marasa godiya, marasa tsarki, marasa kauna irin na tabi’a, masu bakar zuciya, masu tsegumi, marasa kamewa, masu zafin hali, marasa son nagarta, masu ci amana, masu taurin kai, masu kumbura, mafiya son annkshuwa da Allah, suna rike da surar ibada, amma sun musanci ikonta daga wajen wadannan kuma sai ku bijire. Gama irin su masu sanda ne zuwa cikin gidaje, suna bautar da mata marasa wayo, labtattu da zunubai, batattu ta wurin sha’awoyi iri-iri, kullum suna kan koya, ba su kuwa da iko su riski sanin gaskiya daidai ba.” A cikin duk abubuwan da muka karanta yanzun nan, babu daya daga ciki wanda ba ya faruwa a wannan zamani. Mutane da yawa sun manta cewa babu sauran lokaci da yawa kuma ga dukanmu; mutane sun shiga yin shagalinsu; sun manta akwai Allah, sun manta akwai mutuwa. Suna gani kamar su ne suke da ikon rike rayukansu; wannan abin kaito ne, abin kuka kuma. Yesu Kiristi ya yi mana koyarwa a cikin littafin Matta 24 :1- Yesu ya fita haikali, yana cikin tafiya, sai almajiransa suka zo wurinsa domin su gwada masa gine-gine na haikali. Amma ya amsa, ya ce musu, ba ku ga wannan abu duka ba? Hakika, ina ce muku, ba za a rage wani dutse bisa wani ba, da ba za a rushe ba. Yana nan yana zaune bisa dutsen Zaitun, sai almajiran suka zo wurinsa waje daya, suka ce, ka fada mana, yaushe wadannan abubuwa za su zama? Mene ne kuma alamar zuwanka da karshen zamani? Yesu ya amsa, ya ce musu, ku yi lura kada kowa ya bashe ku, gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, su ce, Ni Kiristi ne; za su kuwa bad da mutane da yawa. Kuma za ku ji labarun yakukuwa da zizar yaki: ku yi lura kada hankalinku ya tashi: gama wadannan al’amura dole za su faru, amma matuka ba ta yi ba tukunna. Gama al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki kuma za ya tasar wa mulki: za a yi yunwa da raye-rayen duniya a wurare daban-daban. Amma duk wadannan al’amura mafarin wahala ne. Sa’annan za su mika ku ga kunci, za su kashe ku kuma, za ku zama abin ki ga dukan al’umma saboda sunana. Sa’annan mutane da yawa za su yi tuntube, za su ba da juna, za su ki juna kuma. Kuma masu karyar annabci da yawa za su tashi, su bad da mutane da yawa. Saboda yawaita da mugunta za ta yi kuma, kaunar yawancin mutane za ta yi sanyi. Amma wanda ya jure har matuka shi ne za ya tsira. Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’umma; sa’annan matuka za ta zo.”
’Yan uwana maza da mata, Allah bai bar komai a cikin duhu ba ko kadan game da zancen karshen duniya, babu abin da dan Adam zai iya yi ya canja shirin Ubangiji Allah, Akwai kungiyoyi da dama a cikin wannan duniya a yau, wadanda suke ganin kamar suna da wata hikima wadda za ta iya canja komai ma; daya daga cikin wadannan kungiyoyin ita ce wadda ake kira Majalisar dinkin Duniya; babu abu daya da za su iya dinkewa idan ba nufin Allah ba ne. Wani mawaki a cikin wakarsa ya ce idan sun dinka daga nan; sai can ya farke.
Idan Allah Ya bar mu cikin masu rai zan so in yi bayani kadan a kan wuraren da muka karanta a yau kafin mu shiga koyarwa a kan irin shari’ar da masu bin Yesu Kiristi za su fuskanta bayan an fyauce mu.
Sai mu yi tunani a kan kowace irin rayuwa muke yi a yau? Kada kuma mu manta Allah Ya ba mu aikin yin addu’a domin shugabaninmu su iya yin mulki bisa tafarkin Allah. Mu sa su cikin addu’a musamman Shugaba Muhammadu Buhari. Ubangiji Ya taimake mu, amin.