A ranar Alhamis 25 ga watan Agusta aka a fitar da jadawalin gasar Kofin Zakarun Turai wato UEFA Champions League na kakar 2022/23 da za a fafata a birnin Istanbul na kasar Turkiya.
Karo na 68 da za a gudanar da babbar gasar tamaula ta kungiyoyin zakarun Turai, kuma karo na 31 tun bayan da aka sauya fasalin wasannin.
- Harin bom ya kashe mutum 18 a masallaci a Afghanistan
- Harbo jirgin China da muka yi mataki ne da ya dace —Taiwan
Za a fara gumurzun cikin rukuni a babbar gasar kungiyoyin Turan daga ranar 6 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Yunin 2023.
Real Madrid ce mai rike da kofin da ta lashe a kakar da ta wuce, bayan doke Liverpool a Faransa, ta dauki na 14 jumulla.
Yadda aka raba jadawalin gasar
Ga yadda cikakken jadawalin yake:
Rukunin A: Ajax, Liverpool, Napoli, Rangers
Rukunin B: Porto, Atletico Madrid, Bayer Leverkusen, Club Bruges
Rukunin C: Bayern Munich, Barcelona, Inter Milan, Viktoria Plzen
Rukunin D: Eintracht Frankfurt, Tottenham, Sporting Lisbon, Marseille
Rukunin E: AC Milan, Chelsea, RB Salzburg, Dinamo Zagreb
Rukunin F: Real Madrid, RB Leipzig, Shakhtar Donetsk, Celtic
Rukunin G: Manchester City, Sevilla, Borussia Dortmund, FC Copenhagen
Rukunin H: Paris St-Germain, Juventus, Benfica, Maccabi Haifa
Lokutan da za a buga wasannin
Wasannin farko: Ranar 6 da 7 ga watan Satumba
Wasanni na biyu: Ranar 13 da 14 ga watan Satumba
Wasanni na uku: Ranar 4 da 5 ga watan Oktoba
Wasanni na hudu: Ranar 11 da 12 ga watan Oktoba
Wasanni na biyar: Ranar 25 da 26 ga watan Oktoba
Wasanni na shida: Ranar 1 da 2 Nuwamba
Bayan kammala wasannin rukuni, a ranar 7 ga watan Nuwamba za a raba jadawalin wasannin zagaye na biyu wato zagayen ’yan 16.
Za a soma wasannin zagaye na biyu daga ranakun 14 da 15 sai kuma 21 da 22 ga watan Fabrairun 2023.
Sannan za a buga wasa na biyu daga ranakun 7 da 8 sai kuma 14 da 15 ga watan Maris na badin.
Zagayen Kwata-final: A ranakun 11 da 12 za a buga wasannin zagayen kwata-final, sannan kuma a buga wasannin na biyu a dai wannan mataki a ranakun 18 da 19 Afirilun 2023.
Wasannin daf da na karshe: A ranakun 9 da 10 za a buga wasannin zagaye na farko a matakin daf da na karshe sannan a buga zagaye na biyu a ranakun 16 da 17 ga watan Mayun 2023.
Wasan karshe: A ranar 10 ga watan Yunin 2023 za san kungiyar da za ta zama Zakarar Turai ta 2023.
Farfajiyar da za a buga wasan karshe na gasar Kofin Turai a shekarar 2023
Za a buga karawar karshe a filin wasa na Ataturk a Istanbul, filin da tawagar Turkiya ke buga wasanninta.
Filin ne ya karbi bakuncin wasan karshe a 2005, wanda AC Milan ta ci Liverpool 3-0 daga baya kungiyar Anfield ta farke ta lashe kofin.
Tun farko an tsara cewar filin ne zai karbi bakuncin karawar karshe a 2020 daga baya aka mayar da wasan Lisborn, sakamakon bullar cutar kwarona.
An kara tsara cewar filin ya karbi bakuncin fafatawar karshe a 2021 a Istambul, nan ma aka mayar da wasan Porto, saboda dokar hana yada cutar kwarona.
Shin Real Madrid za ta iya kare kambunta?
Real Madrid ta fara kakar wasa ta 2022/23 da kafar dama, inda ta yi nasara sau hudu a jere cikin wasanni hudu a duk fafatawar da ta yi wadda ta soma da gasar cin kofin UEFA Super Cup, inda ta doke Eintracht Frankfurt.
Daya daga cikin manyan manufofinta a wannan kakar ita ce kare kambun babbar gasar Sfaniya wato La Liga, wani abu da kungiyar ba ta jima ba ta yi ba tun 2008, amma farawa da ci a wasannin da ta fita bakunta zuwa Almeria da Celta Vigo da Espanyol, tabbas zai taimaka wajen kara mata karfin gwiwa da kuma jajircewa kan abin da ta sa gaba.
Tuni dai har kungiyar ta bayar da rata a tsakanin manyan abokan hamayyarta biyu wato Barcelona da Atletico Madrid, wadanda duk sun barar da maki a karawarsu da Rayo Vallecano da Villarreal.
A wannan yanayi, ana iya cewa Real Madrid ta soma kakar wasannin bana da wani karsashi da dade ba ta soma da makamancinsa ba tsawon shekaru.
Tun daga shekara ta 2008, yunkurin da Madrid ta yi na kare kambun La Liga ya zame mata tamkar tarar aradu da ka, inda a wasan farko na kakar wasannin 2008/2009 ta sha kashi, kuma ta karar kakar a bayan Barcelona da tazarar maki 19 tsakani.
Kungiyar ta iya hada maki hudu ne kacal daga cikin maki 12 da take da dama a kansu a kakar wasanni ta 2012/2013, ina a nan ma ta kare La Ligar a bayan Barcelona da tazarar maki 15 tsakani.
A kakar 2017/18, Madrid ta yi canjarasa sau biyu a jere a gida a wasannin mako na biyu da na uku na La Ligar da ta karbi bakuncin Valencia da Levente. A wannan kakar ma dole ta sallama La Ligar wadda ta kare a mataki na uku da ratar maki 17 tsakaninta da Barcelona wadda ta lashe gasar.
Haka kuma a kakar wasanni ta 2021, Real Madrid ta yi gumurzu iya gumurzu tun daga farkon gasar La Liga har zuwa karshenta, sai dai kash ta kare da tazarar maki biyu kacal a bayan Atletico Madrid wadda ta lashe gasar a shekarar. Madrid ta barar da maki biyu wasan mako na farko a fafatawar da ta yi da Anoeta, wanda manazarta harkokin kwallon kafa suka ce wannan wasan ne ya yi tasiri kan kaddarar kungiyar a lokacin.
A duk cikin kungiyoyin da ake ganin su na da duk wata cancanta ta lashe gasar Zakarun Turai ta 2022/2023, Real Madrid ce ta fita zakka kuma ta zama zakaran gwajin dafi a cikinsu.
Alamu sun nuna wannan kaka ita ce kan gaba ta fuskar farawa da kafar dama a bangaren kungiyar musamman idan kwatanta da sauran manyan kungiyoyin Turai.
A halin yanzu dai Real Madrid ce kadai babbar kungiya cikin dukkan kungiyoyi masu fafutuka a gasar zakarun Turai da suka fara taka rawar gani.
Tuni dai Manchester City da Liverpool suka barar da maki a gasar Firimiyar Ingila da a yanzu har an shiga wasannin mako na biyar, yayin da Bayern Munich da PSG su ma ba a barsu a baya ba inda kowacce ta barar da maki a wasannin da suka fafata a karshen makon nan.
A hakikanin gaskiya, sauran kungiyoyin da suka nasara 100 bisa 100 a manyan lig-lig guda biyar na Turai su ne Arsenal wadda ita ba ta cikin gasar Zakarun akarun Turai, sai kuma Real Betis da Los Blancos za ta karbi bakuncinta a filin wasa na Estadio Santiago Bernabeu ranar Asabar a gasar La Liga.
Kungiyoyin da Real Madrid za ta kara da su a zagayen rukuni na gasar Zakarun Turai
A rukunin F dai baya ga Real Madrid, akwai RB Leipzig da Shakhtar Donetsk da kuma Celtic.
Real Madrid mai rike da kambun kofin Zakarun Turai za ta yi karon-batta da abokan hamayya da sabbin kalubale da ba wannan ne farau ba, a yayin da kungiyar ke kokarin lashe gasar karo na 15 a tarihi.
A matsayinta na kungiya mafi nasara a kwallon kafar Turai da tazara babba, Los Blancos a iya cewa tamkar wata Sarauniya ce da ba a cinta da yaki a gasar Zakarun Turai. Kungiyar tana da kofuna 14, martabar da ta ninka ta kowacce kungiya kasancewar AC Milan da biye mata a mataki na biyu ta lashe gasar sau bakwai a tarihi.
Ba a taba fitar da kungiyar a matakin rukuni ba na gasar Zakarun Turan tun bayan da aka kawo tsarin zagayen wasanni rukuni a gasar a shekarar 1995.
Yaya za ta kaya tsakanin Real da sauran kungiyoyin da suke rukuni daya?
RB Leipzig
Kungiyar Leipzig ta Jamus ta zo ta uku a bayan Manchester City da Paris Saint-Germain a rukunin A a bara. Ta samu nasarar kaiwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin Europa kafin su sha kashi a hannun Rangers da ci 3-2.
Shakhtar Donetsk
Madrid da Shakhtar sun hadu a rukunin D a bara. Los Blancos ta samu nasara ce da ci 5-0 a wasan da ta je bakunta Ukraine kafin ta sake lallabo ta zuwa Sfaniya ta kara mata da ci 2-1. A wasan na Karim Benzema ya ci wa Real Madrid kwallo ta 1,000 a gasar kwallon kafa ta Turai. Kungiyoyin sun kuma hadu a kakar 2020/21, lokacin da Shakhtar ta lallasa Real Madrid da ci 3-2 a wasan zagayen farko na rukuni.
Celtic
Madrid da Celtic ba taba haduwa da juna ba tun bayan da aka sabunta gasar Zakarun Turai. A gwajin kwanji na karshe da suka yi a gasar kafin a sauya mata (lokacin ana kiranta European Cup) sun hadu a wasan daf da na karshe a kakar 1979-80, lokacin da kungiyar ta Sfaniya ta kai bantenta zagayen na biyu bayan rashin nasara da ci 2-0 a wasan zagayen farko, inda aka karkare 3-2 jumulla, sakamakon bugun daga kai sai mai tsaron gida da Juanito ya ci.