Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Abdulrashed Bawa, ya yi wata ganawa ta musamman da masu shirya fina-finai na Arewaci da Kudancin kasar nan a ofishin hukumar da ke Abuja.
Hukumar tace fina-finai ta kasa ce ta shirya taron ranar Alhamis, da hadin gwiwar EFCC don a tallata wa duniya abin da hukumar take yi da kuma wayar da kan jama’a abubuwan da za a kiyaye a bisa tsarin doka.
- Kotu ta daure mahaifin da ya yi wa ’yar cikinsa fyade shekara 23
- Amotekun ta sake kama matafiya ’yan Arewa 151 a Ondo
A hirarsa da Aminiya, Dokta Ahmed Sarari, shugaban kungiyar masu shirin fim ta MOPPAN wanda ya halarci taron, ya ce, “Hukumar na so masu shirin fim su yi amfani da irin hukunce-hukunce da suka yi na shari’oi na cin hanci da rashawa a fina-finai don fadakarwa.
“Domin cim ma wannan buri, hukumar ta amince ta da samar da wani sashe wanda zai kula da wannan aiki na kyautata alaka da ‘yan fim a karkashin bangaren hulda da jama’a.
“Aikin wannan sashe ya hada da kirkira, da bayar da bayanai, da taimakawa duk mai son yin fim dangane da ayyukan hukumar yadda ya kamata, kamar yadda ake yi a fina-finan waje,” inji Dokta Sarari.
Dangane da aiwatar da wannan aikin, ya ce tuni aka kafa kwamitin da zai shigar da wannan bukata ga hukumar a rubuce ya kuma mika mata nan da ranar Litinin mai zuwa.
Taron na yini daya ya samu halartar shugabannin kungiyoyin masu shirya fina-finai na Kannywood da kuma Nollywood.