Majalisar Dokokin Jihar Borno ta musanta zargin da ake mata na yunkurin tsige Gwamna Babagana Zulum, a ranar Alhamis.
Martanin ya fito daga bakin Shugaban Majalisar, Abdulkarim Lawan, jim bayan zaman gaggawa da suka yi a Maiduguri, kafin dage zaman Majalisar zuwa ranar 1 ga Afrilu.
- An kama mata ta boye kunshin kwaya 18 a al’uararta
- Farashin fetur zai kai N234 bayan cire tallafi
- Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Kamaru 2 a Borno
- Zulum zai tura dalibai kasar waje domin karatun aikin likita
“Babu wani shiri da majalisa ta yi na tsige jajirtaccen gwamnanmu, wanda ya dawo mana da martabarmu.
“Mun yi alawadai da wannan labarin kanzon kuregen da aka yada a kafafen sada zumunta.
“Muna shawartar kafofin yada labarai da su kasance masu tabbatar da labari kafin su yada.
“Kuma muna kira ga jami’an tsaro da su yi aikinsu wajen gano wanda ya fara asassa wannan labarin, domin hukunta su.
“A matsayinmu na ’yan Majalisar Jihar Borno muna tare da gwamnanmu, Babagana Umara Zulum, dari bisa dari,” cewar Lawan.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Dige Mohamed, tund a farko ya shawarci Majalisar ta yi doka game da irin abubuwan da ake wallafa wa a shafukan sada zumunta.
A ranar Alhamis ne dai, labarin tsige gwamnan ya fara karade kafafen sada zumunta, wanda wata jarida ta wallafa.