Masana’antar Kannyood ta dade tana fama da rikice-rikice, musamman tsakanin jarumai da furodusoshi da sauransu.
A lokuta da dama rikice-rikicen kan zo wa wasu a matsayin abin mamaki, amma kuma a wajen wasu musamman wadanda suka san yadda ake tafiyar da harkokin masa’antun fina-finai na duniya ba sabon abu ba ne.
Daga cikin rikice-rikicen da aka sha fama da su a Kannywood akwai yadda danganta ta yi tsami tsakanin jarumi Ali Nuhu da Adam A. Zango wanda shi ne ya fi fitowa fili.
Sai kuma alamun sabani tsakanin bangarorin masana’antar da dama, wadanda a sau tari ba sa nunawa, amma ayyukansu ke fito da su.
Asalin rikicin Ali Nuhu da Zango
A shekarar 2019 ce dai Ali Nuhu ya maka Adam A. Zango a kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge, a Kano bisa zargin sa da bata masa da cin mutunci.
Wannan ne kololuwar tsamin dagantar a tsakaninsu, wanda shi kan shi Adamu a lokacin ya ce ya ba shi mamaki kasancewar ko sunan dansa na farko Ali ya sa ne saboda alakarsa da Ali Nuhu.
Sai dai daga baya an musu sulhu kafin a shiga kotun, inda Salisu Mu’azu ya jagoranci sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar wajen sulhun.
Kafin wannan, an sha samun sabani da rikici a tsakanin jaruman guda biyu, ana musu sulhu.
A watan Fabrairun 2014 lokacin jaruman suna da kusan shekara 14 da kasancewa tare a masana’antar ce Zango ya fito ya bayyana wa duniya cewa ya yanke alakarsa da Ali Nuhu.
Rikicin ya yi zafi ne a shekarar bayan jaruma Rahama Sadau ta shiga shafinta na Instagram ta yi wa Zango maganganu marasa dadi saboda ya cire ta a fim dinsa mai suna Duniya Makaranta.
Daga baya Rahama ta ba shi hakuri, amma duk da haka rikicin ya ci gaba da zafi bayan da fitaccen mai barkwancin, wanda a lokacin yake karkashin Adam A. Zango wato Ali Artwok wanda ake wa lakabi da Madagwal ya fito ya caccaki Ali Nuhu.
Nan suma yaran Ali Nuhu a wancan lokacin, irinsu Garzali Miko da Shamsu Dan’iya da sauransu suka kai karar Ali Artwork, inda ’yan sanda suka neme shi amma ba su same shi ba. Nan aka kama mahaifiyarsa, daga baya ya kai kansa.
Bayan wannan ne Zango ya fito ya ce da ma shi ya daura wa kansa sunan yaron Ali Nuhu kuma yake cewa ubangidansa ne amma ba hakan ba ne.
Ya ce shi ya fara yi wa kansa fim, kafin wani ya yi masa bayan sun ga kwazonsa.
Fim din da ya yi wa kansa a lokacin shi ne Surfani, sai furodusa Bauni ya masa Dukiya, Ali Nuhu ya masa Zabari.
Adamu ya sha yin zargin cewa Ali Nuhu yana sa yaransa su zage shi, zargin da Ali Nuhu ya musanta inda ya taba cewa a tambayi Zango din lokacin da yake karkashinsa ko ya taba sa shi ya zagi wani.
Yadda Ali Nuhu da Zango suke a yanzu
Tun bayan wancan rikici da har ya kai ga zuwa kotu, sai aka samu zaman lafiya amma daga nesa-nesa.
A lokacin bikin zagoyowar ranar haihuwar Adam A. Zango, Ali Nuhu da yaransa irinsu Khaleed Yusuf da darakta Sheikh Isa Alolo da sauransu, duk sun fito sun taya shi murna.
Shi ma Zango ya rika taya Ali murna ko jaje a duk abubuwan da suka shafi Alin.
Amma a watan Nuwamban 2020 ne zumuntarsu ta kara fitowa fili bayan da Adam A. Zango ya sanya hoton Ali Nuhu, inda ya ce sarki, sarki ne, sannan ya kara da cewa ba a canja wa tuwo suna, lamarin da ya faranta wa masoya bayansu rai matuka.
Dama can akwai yaron Zango na gaba-gaba, Mansur Make Up, wanda a lokuta da dama yakan yawan yi maganar cewa yana so a samu hadin kai a masana’antar, kuma ko lokacin rikicin, bai daina bibiya tare da taya Ali Nuhu murna ko jaje ba a duk abubuwan da suka same shi.
Daga baya Zango ya kara sanya hoton Ali Nuhu, inda ya bayyana cewa suna samun sabani, amma yadda suke shiryawa su wuce wajen kamar ba a yi ba ne ya nuna cikarsu. A nan ma ya sake kiransa da Sarki.
A nan ne shi ma Ali ya sanya hoton Zango, inda ya nuna cewa Adamu abokinsa ne kuma dan uwansa ne, sannan ya yi godiya kan kasancewarsu tare, ya kuma yi fatar su ci gaba da kasancewa taren. Sannan ya kira shi da yarimansa.
Wannan al’amari ya faranta wa masoya rai, ciki har da marubuci Abdulkareem Papalaji, wanda ya dade su biyun, inda ya rubuta cewa an zo wajen.
Shi ma furodusa Naziru Danhajiya cewa ya yi sarki ya magantu, sannan ya nuna farin cikinsa.
Haka kuma, Zango ya je kallon fim din Fati, na furodusa Abubakar Bashir Maishadda, inda a nan aka yi ta nuna shi tare da Ali Nuhu suna hira a sinima da ke Kano, sannan daga sinimar Adamu ya je shagon sayar da kaya na Ali Nuhu domin ziyara.
Kasancewar idan Ali Nuhu da Zango sun samu sabani, masana’antar takan rabu biyu ne, wasu suna bayan Ali wasu na bayan Zango, sai ’yan tsaka-tsakiya kuma; Hadin kansu, zai dinke matsaloli da dama a masana’antar.
Dama can masu sharhi a kan al’amuran Kannywood suna ganin abin da ke kawo rikicin shi ne yadda yaran Zango suke masa lakabi da Sabon Sarki, su kuma yaran Ali Nuhu suke ganin Sarki daya ne, amma sun amince Zango ne yarima.
Amma yanzu akwai alamar cewa an dinke wannan barakar, ganin Zango ya kira Ali sarki, shi kuma ya kira shi yarima.
Ali Nuhu ya kai ziyara Tamil
A wani mataki na kara samun sulhu, Ali Nuhu da Darakta Sanusi Oscar 442 sun shammaci mutane bayan da daraktan ya sanya hotonsa da Ali Nuhu, sannan ya ce, “muna godiya da ziyarar ambasada Ali Nuhu.”
Shi ma Ali Nuhu ya yada hotunan ziyarar tasa, a lamarin da aka dade ba a ga irinsa ba tsakanin Ali Nuhu da Oscar a Kannywood.
Wannan ziyarar tana da matukar muhimmanci, domin ana ganin darakta Sanusi Oscar da Ali Nuhu ba sa ga maciji, duk da cea suna kasance a tare a da.
A watan Nuwamban 2020 ne Ali Nuhu ya sanya Mommee Gombe, wadda a yanzu kusan ita ce babbar jarumar Tamil da ke jan zare a fim dinsu mai suna Zainab Abu.
Tun bayan nan ake tunanin akwai rina a kaba sannan kafin nan ma, Ali Nuhu ya taya ta farin cikin ranar haihuwarta, wanda wasu da dama suka yi mamaki.
Tamil Nadu wani bangare ne a masana’antar Kannywood, karkahin darakta Sanusi Oscar, inda yake kokarin kawo sauyi a masana’antar.
A wata zantawa da ya yi da Aminiya a kwanakin baya, daraktan ya ce yana kokarin komawa YouTube ne saboda ya hango cewa zamani ya canja, kuma dole rika tafiya zamani idan ana so a ci gaba da kasancewa da kima.
Shi ne ya ba da umarni a wakar Jaruma ta Hamisu Breaker wadda ta yi fice matuka a cikin kankanin lokaci.
Kasancewar darakta Sanusi Oscar yana renon matasan jarumai, hadin kansa da sauran furodusoshi da daraktoci zai taimaka wajen kawo sababbin fuska a masana’antar da cigabanta.
Yadda nuna fim din Fati ya hada kan mutane da dama
Haka ma a wajen nuna fim din Fati, an samu wani irin hadin kai, inda bangarorin masana’antar da dama suka zo kallo.
Daga cikin wanda ya dauki hankalin mutane akwai Furodusa Alhaji Mustapha Ahmad wanda aka fi sani da Alhaji Sheshe, wanda ya zo kallon fim din ba ma sau daya ba.
A shekarun baya ne Alhaji Sheshe ya biya Ali Nuhu Naira dubu 500 don ya rage gashin kansa saboda rawar da zai taka a fim dinsa mai suna ‘Kazamin Shiri’.
Sai dai zuwan Alhaji Sheshe sinima domin kallon fim din Fati, sannan aka yi ta nuno su tare da Maishadda ya sa masoyansu sun cika da farin ciki.
Hadin kai tsakanin manyan furodusoshi zai taimaka matuka wajen kawo cigaba a masana’antar.
Hakanan shi ma Ali Artwork da Hamza Talle Maifata daga Jos da sauransu duk sun halarci kallon fim din, wanda hakan ke nuna fim din ya zama wajen sada zumunci da sulhu.
Fati, fim din Ali Nuhu, wanda Abubakar Bashir Maishadda ya shirya, darakta Kamal S. Alkali ya ba da umarni, sannan Umar M. Shareef da jaruma Fatima Usman Kinal suka ja shirin.
Haka kuma, kotu ta sallami shari’ar Naziru Sarkin Waka da ta darakta Sanusi Oscar 442.
Wannan shi ma ana ganin ba ya rasa nasaba da yunkurin samar da sulhu da zaman lafiya a Kannywood.
Zaman lafiya ya fi zama dan sarki —Muhsin Ibrahim
Aminiya ta tuntubi Malam Muhsin Ibrahim, wanda malami ne a Jami’ar Cologne da ke Jamus, wanda kuma mai sharhi ne a kan al’amuran da suka shafi masana’antar Kannywood, inda ya ce ai dama zaman lafiya ya fi zama dan sarki.
A cewarsa, “Ni ma na kula da kokarin hadin kan da yake gudana a Kannywood.
“Wannan abu ne mai matukar kyau, domin zai samar wa da masana’antar cigaba kusan ta kowanne bangare. Zaman lafiya, ya fi zama dan sarki, inji masu iya magana.”
Malamin, wanda shi ne mawallafin littafin Kannywood: Unveiling the Overlooked Hausa Industry, ya kara da cewa, “Misali, hakan zai kawo zabar jaruman da suka cancanta lokacin yin fim (casting).
“Da kawai ana duba cewar ina shiri ko ba na shiri da wane, wanda hakan ba shi da kyau. Da dai sauran al’amura.
“Kamar yadda na ce, muna maraba da wannan abun. Allah Ya kara hada kawunansu, amin.”