Al’ummar Karamar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato sun karyata labarin nutsewar jirgin ruwa dauke da ’yan bindiga kimanin 200 a yankin.
Wasu kafofin labarai dai sun ruwaito cewa jirgin ruwa dauke da yan bindiga kimanin 200 ya nutse da su a yankin na Sabon Birni.
Al’umma sun bayyana cewa ba wani rahoto mai kama da wannan a yankin nasu.
Wani da asalin yankin Sabon Birni, Muhammadu Danmutune, ya shaida wa wakilinmu cewa bai samu wanna labarin ba kuma ya bincika sosai babu wannan maganar a yankinsu.
- Babu wanda aka kashe a zanga-zangar yunwa a Kano —’Yan sanda
- Zanga-zanga: ’Yan Sanda sun cafke mutum 873 a Kano
- An sace N50bn daga asusun Gwamnatin Kano —Muhyi
“Wuraren da muke da gulabe a Sabon Birni kamar Kurawa, Tara, Gatawa, Dinkawa, Akallawa da Gangara.
“Sai ƙananan gulabe a Takatsaba, Unguwar Lalle, Lajinge, dukansu babu wannan labarin da ake yadawa.
“Haka muka gani a kafafen yada labarai na zumunta ana yadawa, magana ta gaskiya babu sahihanci kan labarin da ake yadawa.
“Maganar ’yan bindiga sun nutse abu ne mai girma, in da ya faru da yanzu an san wurin da ya faru kuma za a ga ko da gawar mutum daya ne.
“Amma ka ga mutum 100 ake magana sun nutse, labarin nan bai faru ba,” a cewar Danmutune.
Bashar Altine, Shugaban Rundunar Adalci ta Kasa, wanda shi ma dan yankin ne, shi ma ya ƙaryata maganar.
A hirarsa da wakilinmu, ya ce ba su da gulbin da zai iya daukar jirgin da mai daukar ko da mutum 50 ne a lokaci guda a yankin.
Ya ce labarin karya ne ake bazawa a gari, don haka mutane su fita batun zancen, bai inganta ba.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i, bai yi nasara ba, domin jami’in bai amsa kiran wayansa ba.