“Wasila” daya ne daga cikin fina-finan Hausa da suka shahara a farko-farkon shekarun 2000.
Daya daga cikin abubuwan da suka sa fim din ya shahara kuma ita ce wakar fim din, “Wasila kin ci amanita”, wadda Ghalin Money ya rubuta, ya kuma rera.
Sai dai shekara da shekaru an daina jin muryar mawakin ko a fina-finai ko ma a fagen waka gaba daya.
Aminiya ta tattauna da shahararran mawakin domin jin ina ya shiga aka daina jin duriyarshi, dama wasu batutuwan game da rayuwarsa.
Aminiya: Wane ne Ghalin Money?
Ghalin Money: Sunana Muhammad Ghali Yusuf, wanda aka fi sani da Ghalin Money, kuma dalilin lakabin Ghali Money shi ne kanin mahaifina wanda na taso a hannunsa – mutane na kiransa da wannan sunan, don haka sai ni ma ana kirana da lakabin Ghalin Money.
Ka ji asalin sunan. Kuma ni haifeffen Zariya ne a Jihar Kaduna.
Na fi karfi ta fannin karatun addini domin da Allah Ya sa na kammala makarantar Jama’atu ta Kofar Fadar Sarkin Zazzau, sai na tafi kasar Masar don na yi karatun addini.
Ina Galin Money ya shiga ba a jin duriyarshi na wani lokaci?
To dalilin shi ne rayuwa; domin ka san rayuwa tana zuwa iri-iri, to kuma sai yadda Allah kuma Ya so da bawanShi.
Kuma ba wakar na ajiye ba, domin na yi wakokin talla da dama.
Da na dan huta ne to amma ai ka ga na yi wakokin talla irin na su Dangote da MTN da dai sauransu; wakar ce dai na dan kwana biyu ban yi ba saboda wasu dalilai.
Ka shahara da wakokin Hausa fim – yaya aka yi ka fara, a ina, kuma yaushe?
Haka ne to da ina wakokin yabon Mazon Allah (SAW) ne, wakar mandiri nake yi.
To a lokacin da na fara wakokin fim a garin Kano ne; akwai wani kamfani mai suna Jari Film Production wanda muke zuwa muna daukar kaset na bidiyo, wanda kuma ina da wani yayana wanda shi ke da wurin. A lokacin sai suka yi sha’awar za su yi fim, to sai suka gayyace ni cewa don Allah in zo in yi musu waka, to a wannan lokacin shi ne na fara shigowa harkar fim.
Wakokin fim nawa ka yi?
Ah wannan tambaya ba za ta amsu ba don na yi wakoki da yawa, kuma a lokacin ba lissafinsu nake yi ba.
Misali ka ce ka yi wakar fim kaza ba, sai dai suna da dan dama wanda ba zan iya cewa ga adadinsu ba.
Wacce ce ta farko?
Wakata ta farko a fim ita ce waka mai suna “Tagwayen Soyayya” wadda na rera ta a kamfanin Jari Film Production a fim din da suka shirya.
Wacce ce ta karshe?
To idan a wakokin da na yi a fim ne ba zan iya tunawa ba, amma in dai kuma a fagen waka ta yau da kullum ne to akwai wata waka da na rera ta a kwanan nan mai suna “Mutum”.
Wacce waka ce a ciki ta fi burge ka? Me ya sa?
To ni ba wai wakar fim, ko wata waka ba, a kullum ni abin da ya fi burge ni shi ne kirkira, watau kamar na yi wani sabon abu, sai kuma yin wasu abubuwa wadanda ko bayan ba ka zai zama darasi ga mutane, kamar wakoki na fadakarwa da wakoki na tunasar da mutane. To na fi sha’awar irin wadannan wakokin; su ne suka fi burge ni.
Ka daina waka ne ko wakokin fim ka daina?
A’a, ban daina waka ba tun da yanzu ma ai wakar wakar ce ta jawo ku, ka ga ai ba a daina waka ba sai dai wakar fim ita ce na dade ban yi ba saboda dan wani hutu da na dauka a dan wannan barayin a kai, amma akwai wakoki musamman a kan siyasa na wayar da kan jama’a a kan zaben da ya gabata na 2019 din nan.
To wace waka ce ka yi ta karshe a cikin wakokinka?
Eh a cikin wake-waken da aka yi na fina-finai ba zan iya tunawa da wakar da na yi ta karshe ba saboda a gaskiya an dan dauki lokaci mai tsawo; don daga lokacin da na daina wakar fim zuwa yanzu za a sami kusan shekara 15.
To a cikin wakokin da ka yi wacce ce ta fi fice?
To wakar da ta fi fice ai kowa ya sani ita ce wakar “Wasila”.
Wannan waka ita ce ta fi fice a cikin wakokin da na yi, kusan ita ce za a ce bakandamiya a wakokina da kowa ya sani a film din “Wasila” kashi na daya da na biyu—dukkan wakokin ni na yi su.
Mene ne burinka game da wake-wake?
Burina ga wake-wake shi ne ya zamana cewa a rika tsaftace harkar, kuma ba wai a dauki harkar waka ta bangaren wasanni ba kawai.
Waka wata baiwa ce wadda ba kowa Allah Yake ba ba, kuma waka tana da hanyoyin da za a jawo hankalin jama’a ta ko wane bangare—abin da ya shafi harkar tsaro ne, ilimi ne, da noma da kuma harkar zamantakewa ta mata da miji.
Ga dai abubuwa nan da dama domin duk bangaren da ka zauna ka yi tunani a kanshi za ka iya hada waka, don haka ne ni babban burina shi ne wakar fadakarwa kafin a ce za a yi ta shargalle.
Yaushe za a sa ran sake jin ka a fagen waka?
Eh game da wakar fina-finai to wannan ban san ma lokacin da za a ce za a sa ran na dawo ba, saboda harkar ta canza ba irin yadda ake yi da ba ne; kuma kowane tsutsu an ce kukan gidansu yake yi.
Don haka dole idan ka ga wani abu wanda kake tunanin cewa zai ba ka matsala a rayuwarka ko a bayan rayuwarka—mutum ya bar abu mai kyau ga zuri’arsa don haka a aiki ka ga dole ne ka yi taka-tsan-tsan.
Amma ai wakoki yanzu aka fara yin su musamman irin na fadakar da al’umma; ba ga shi yanzu za mu yi waka a kan mutum da irin halayyarshi da kuma yadda mutum yake da mugun hali ba?
To nan gaba kuma in Allah Ya yarda za mu yi wakar da za mu fitar da halayyarsa mai kyau domin mu yi daidaito a wakar domin yanzu idan ka tara mutane, da yawansu sai ka ga cewar su a wanke suke ba su da wani aibi a tattare da su.
To shi ya sa muka fara rera wakar fadin abu mara kyau a kan wasu daga cikin halayyar mutum kafin fadin mai kyau don mu yi adalci a cikin alhairan shi mutum.
Ka dauki tsawon shekaru nawa a yazu kana harkan waka?
To da fara waka—yanzu akalla na kai shekara 33 ina waka. Domin tun ina da shekara 16 na fara waka yanzu shekaruna 49.
To maganar iyali fa, ka cike ne ko akwai sauran kofa?
(Dariya) A’a, ka san ni Bazazzagi ne don haka ina da mata biyu, yara na 15—ka ga ai da sauran kofa kamar yadda ka ce.
To ka san duk abin da mutum ke yi a rayuwarsa wata rana akwai farin cikin da ba zai taba mantawa da shi ba. Mene ne naka?
Eh to ai babban abin jin dadi a duk wata harkar da ka shigo shi ne ya zamana duk abin da mutum yake so ya same shi.
Ni nawa shi ne na sami daukaka ta wannan fannin sana’ata kuma shi ne Allah Ya ba ni domin yanzu duk inda na je da inda na sani da inda ban sani ba an san ni.
Ka ga ai sai dai kawai a yi wa Allah godiya domin hatta tsaro na mutunci mutum ya samu.
Kuma baya ga haka an sami arziki wanda ba ya musaltuwa, mata, zuwa aikin Hajji, motar shiga duk an samu.
Alhamdudillahi, babban arzikin a wurina wanda ba zan taba mantawa da shi ba shi ne na jama’a da Allah Ya ba ni kuma ya sa musu kauna ta.
To wane akasi aka samu wanda ake tunawa da shi?
Akasi ai duk wanda aka ce ya daukaka ai dama ba zai rasa matsaloli ba, domin kusan girman daukakarka to kusan girman matsalarka ke nan; don wasu da ke jikinka ne ma matsalarka.
Don haka akwai kalubale da dama sai dai Allah Ya iya mana kawai.
Yaya alakarka da sauran mawaka ’yan uwanka, kuma wanne ne kuka fi shakuwa?
To akwai alaka mai kyau tsakanina da sauran mawaka ’yan uwana duk da dai ban cika shiga tarayyar waka da wani ba amman dai ni ba ni da wata matsala da duk wani mai sana’a irin tawa.
Yadda muke mutunci da kowa a baya haka ma yanzu. Kuma a cikinsu wanda muka fi shakuwa da shi shi ne Auwal Yakini, ga shi nan kusa da ni.
Shi ne mawakin da muka fi shakuwa da shi, kuma shi ma yanzu wakokinshi suna fita ana saurarensu kuma shi ya fi ga wakar fadakarwa duk da wakar soyayya mu ai shehinanta ne.
Cikin mawaka na da ko na yanzu wanne ne ka fi sauraren wakarsa?
To na farko dai ban ma san shi ba; shi ne Jankidi. Sai Shata sai kuma Dan Anace—su na fi son jin wakarsu.