✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin ina jirgin ‘Nigeria Air’ ya shiga?

Jirgin ya yi batar dabo, domin kuwa an neme shi an rasa.

Rahotannin na nuna cewa sabon jirgin ‘Nigeria Air’ da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya gabatar wa jama’a kafin karewar wa’adin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi batar dabo, domin kuwa an neme shi an rasa.

Yanzu haka dai mutane na ta cece-kuce dangane da inda jirgin ya shiga da kuma lokacin da ake saran ya fara aikin dibar jama’a, tare da neman shafinsa na intanet da zai baiwa jama’a damar sayen tikiti kai tsaye.

Binciken da Daily Trust ta gudanar ya nuna cewar tuni jirgin ya koma cikin tawagar jiragen ‘Ethiopian Airlines’ inda aka dauko shi domin ci gaba da gudanar da zirga zirgar da ya saba yi.

Binciken da jaridar ta yi a ranar 1 ga watan Yuni, ya ce an ga jirgin kirar Boeing 737-860 yana zirga zirga tsakanin biranen Addis Ababa da Mogadishu kamar yadda na’urar zirga zirgar jiragen saman da ake amfani da shi ya nuna.

Rahotan binciken ya ce an kwashe kwanaki 4 ana sauya fasalin jirgin domin mayar da shi cikin jerin jiragen Habasha bayan sauya fentin da aka yi masa da kuma bikin nuna shi a birnin Abuja.

Bayanai sun ce tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya yi kokarin amfani da karfin mulki wajen tilasta hukumomin da ke kula da sufurin jiragen sama a Najeriya su amince da jirgin da kuma ba shi lasisin gudanar da aiki ba tare da bin ka’ida ba, kamar yadda Babban Daraktan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (NCAA), Kaftin O.O. Lawani ya yi zargi, a wata wasika da ya rubuta.

Wakilinmu ya yi kokari domin jin ta bakin ma’aikatar sufurin jiragen saman Najeriya dangane da makomar jirgin ‘Nigeria Air’, amma shugaban sashen hulda da jama’a na ma’aikatar, Odatayo Oluseyi ya ki cewa uffan dangane da lamarin, yayin da Majalisar Wakilai ta gayyaci babban sakataren ma’aikatar sufurin jiragen sama domin yi mata bayani akan halin da ake ciki.

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun ce babu wani jami’in hukumomin Najeriya da ke magana akan makomar wannan jirgi, kuma duk kokarin da wakilinmu ya yi domin samun karin haske akan lamarin, abin yaci tura.