Sakamakon rage farashin man fetur a Najeriya, dillalai na bayyana shirinsu na sayar da man a kan sabon farashin.
A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da rage farashin litar man fetur zuwa naira 21.50 daga naira 125.50
Darekta Janar na Kungiyar Manyan Dillalen Mai ta Najeriya (MOMAN) Clement Isong ya ce kungiyar ba ta yi mamakin rage farshin ba, kuma za su sayar da man a kan sabon farashin.
Ya shaida wa Aminiya cewa ya ce gwamnati ta riga ta sanar da su cewa yanayin kasuwa ne zai rika yanke farashin kayan.
- Gwamnatin Tarayya ta sake rage farashin mai zuwa N121.50
- An sassauta dokar hana ibada a masallatai da coci-coci
- Bude makarantu: Muna duba yiwuwar karkasa azuzuwa — Gwamnati
A nata bangaren kungiyar direbobi ta NURTW ta yaba da rage farashin man, tana mai cewa zai rage tashirin da annobar coronavirus ta yi wa aljifan mambobinta.
Sakataren Kungiyar Kwamaret Tony Asogwe ya bukaci gwamnati ta duba yiwuwar bude sufuri tsakanin jihohi.
Yin hakan a cewarsa na da muhimmanci saboda akasarin ‘yan kasar na yin safara da tafiye-tafiye ne ta kan tituna.
A watan Maris ne gwamnati ta rage farashin man fetur daga naira 145 zuwa naira 125, kafin ta kara ragewa zuwa naira 123.50 bayan makonni biyu.